Connect with us

News

SOKOTO: Hare-haren Ƴan Ta’adda Sun Tilasta Mazauna Ƙauyuka 21 Tserewa Daga Gidajensu

Published

on

Aƙalla mazauna ƙauyuka 21 dake jihar Sokoto Najeriya 21 ne yanzu haka suka gudu daga gidajen su, sakamakon ci gaba da kai hare haren ƴan ta’adda waɗanda ke musguna musu.

Rahotanni sun ce wasu daga cikin mazauna waɗannan ƙauyuka na kwana a daji domin kare kan su daga azabar waɗannan ƴan ta’adda da suke kashe mutane ba tare da ƙauƙautawa ba, yayin da suka haƙura da duk wani alkawarin kai musu ɗauki daga wurin hukuma.

Advertisement

Jami’an EFCC Sun Cafke Mutane 31 Da Ake Zargi Da Damfara Ta Intanet A Abuja ‎

Jaridar  Daily Trust ta bayyana waɗannan garuruwa da suka haɗa da Godan Kare da Kaware da Chabi da Dattabi da Janwake da Sha Rana da kuma darbekami.

Advertisement

Sauran sun haɗa da Gidan Sule da Kuruwa da Mahuta da Dantayawa da Kawala da Bagirbe da Tsatsagi da Katsira da Imasa da Bela da Hura Girke da Galadimmai da kuma Asha Ruwa.

Jaridar ta ce wasu daga cikin mazauna waɗannan garuruwa sun samu mafaka a garin Tureta da ƙauyukan ta, inda suke rayuwa cikin mawuyacin hali, saboda yawan su wanda ya haifar da ƙarancin abinci da kuma rashin kayan more rayuwa.

Advertisement

Wabi mazaunin garin ya ce akasarin ƴan gudun hijirar sun samu mafaka ne a gidan ƴan uwan su maimakon sansanin ƴan gudun hijira, yayin da wasu kuma suka samu mafaka a makarantar firamaren Abdulbaki dake Tureta, inda yawan su ya kai dubu guda.

Jihar Sokoto, musamman yankin Sabon Birni da Isa na fama da matsalar ƴan ta’adda waɗanda ke afkawa jama’a ba tare da samun kariyar jami’an tsaro ba.

Advertisement

Idan ba’a manta ba, waɗannan ƴan ta’addan da suka hana yankin zaman lafiya ne suka hallaka Sarkin Gobir bayan sun yi garkuwa da shi na wani dogon lokaci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending