Opinion
Rikicin CSO A Kano: Lokaci Ya Yi Na Haɗin Gwiwa Domin Kare Manufofin “Kano First”
Daga Comrade Abbas Ibrahim
Rikicin da ya ɓarke a cikin Ƙungiyar Ƙungiyoyin Fararen Hula ta Kano (Kano Civil Society Forum), na ci gaba da jawo ce-ce-ku-ce da damuwa a tsakanin masu ruwa da tsaki da al’ummar jihar, musamman yadda ake kallon ƙungiyoyin fararen hula a matsayin masu kare muradin jama’a da faɗar gaskiya.
Saɓanin da ya fara kan batun maye gurbin shugabanci, yanzu ya rikide zuwa zarge-zarge, rabuwar kai, kafa ɓangarori har ma da garzayawa kotu. Lamarin ya ƙara ɗaukar hankali bayan da ake zargin wasu muradun siyasa sun fara yin tasiri a cikin harkokin ƙungiyoyin da ya kamata su kasance masu cin gashin kansu.
Rushewar Gini Yayi Sanadiyyar Mutuwar Mutum 5 A Abuja
A mafi yawan lokuta, ana kallon ƙungiyoyin fararen hula a matsayin ginshiƙi wajen ƙarfafa dimokuraɗiyya, tabbatar da gaskiya da riƙon amana tare da kare haƙƙin talakawa. Sai dai idan irin waɗannan ƙungiyoyi suka shiga rikicin cikin gida da fafatawar neman iko, akwai barazanar da hakan ka iya yi wa mutuncinsu da kuma aikin da suke yi wa al’umma.
Ko shakka babu, samun saɓanin ra’ayi a kowace ƙungiya abu ne da ba za a rasa ba, musamman a tsarin dimokuraɗiyya. Amma idan rikici ya kai matakin da zai haddasa tsattsauran rabuwar kai da gaba mai ɗorewa, to akwai buƙatar a zauna domin samar da fahimtar juna da sulhu.
Masu bibiyar al’amura da dama na ganin rikicin da ya dabaibaye ƙungiyoyin fararen hula a Kano ya fara wuce gona da iri, inda wasu ke ganin lamarin yanzu ya koma fafatawar nuna ƙarfi tsakanin ɓangarori daban-daban.
Abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda ake danganta wasu daga cikin ɓangarorin da alaƙar siyasa, lamarin da ka iya rage amincewar jama’a ga ƙungiyoyin da ake sa ran za su kasance masu wakiltar muradin talakawa ba tare da son rai ko biyayya ga wata jam’iyya ba.
A baya-bayan nan dai, an yi maraba da sabon yanayin sulhu da haɗin kai a siyasar Kano wanda ya haifar da taken “Kano First”, wato fifita muradin Kano sama da bambance-bambancen siyasa ko son kai.
Wannan sabon yanayi ya sa wasu ke tambayar cewa, idan ’yan siyasa za su iya ajiye saɓani domin ci gaban Kano, me zai hana ƙungiyoyin fararen hula su ma su rungumi zaman lafiya da haɗin kai?
Masu sharhi na ganin taken “Kano First” bai kamata ya tsaya a kan dandamalin siyasa kawai ba, illa ya kamata a ga tasirinsa a aikace, musamman a tsakanin ƙungiyoyin fararen hula da shugabannin al’umma.
Haka kuma, ana ci gaba da kira ga dattawa, masu ruwa da tsaki masu zaman kansu da gwamnatin Kano da su shiga tsakani domin samar da mafita da hana rikicin ƙara faɗaɗa.
A cewar masu wannan ra’ayi, shiga tsakani domin sulhu ba katsalandan ba ne, illa wata hanya ce ta kare haɗin kai da martabar ɓangaren da ke taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa shugabanci nagari da ci gaban al’umma.
Sun bayyana cewa abin da ya kamata a fi bai wa muhimmanci ba wai sanin wanda ya yi nasara ko wanda ya sha kaye ba ne, sai dai yadda za a dawo da amincewa tare da haɗa kan ƙungiyoyin domin ci gaban Kano.
A daidai lokacin da jihar Kano ke fuskantar ƙalubale da dama na ci gaba da zamantakewa, ci gaba da rikicin cikin gida a tsakanin ƙungiyoyin fararen hula ba zai amfani jama’a da komai ba.
Lokaci ya yi da kowane ɓangare zai nuna dattako, haƙuri da sadaukarwa domin samar da zaman lafiya mai ɗorewa. Domin kuwa tattaunawa da mutunta juna su ne mafita mafi ɗorewa ga kowace irin matsala.
Abbas Ibrahim na rubutu daga Kano, kuma ana iya tuntubarsa ta adireshin email: abbasibrahim664@gmail.com
