News
Majalisar wakilai Ta Amince Da Kudirin Kafa Ƴansandan Jihohi
Majalisar wakilai ta amince da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman kafa rundunar ‘yansandan jihohi a Najeriya.
An amince da kudirin ne a zaman majalisar na ranar Alhamis bayan ‘yan majalisar sun kada kuri’ar amincewa da shi.
Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Gwamnan Kano Da Grandi Khadi Akan Alaƙalin Hukumar Hisba Sani Tanimu
Amincewar da majalisar ta yi da kudirin na daga cikin muhimman matakan da ake dauka wajen sauya tsarin tsaro a kasar, inda jihohi za su samu damar kafawa da gudanar da rundunonin ‘yansandansu tare da hadin gwiwa da hukumomin tsaron tarayya.
Masu goyon bayan kudirin na ganin cewa kafa ‘yansandan jihohi zai taimaka wajen inganta tsaro da magance kalubalen rashin tsaro da ke addabar sassa daban-daban na kasar nan.
Sai dai kafin kudirin ya zama doka, har yanzu akwai wasu matakai na doka da kundin tsarin mulki da ya kamata ya bi.
