News
Ana Zargin Wata Amarya Ta Hallaka Mijinta Da Wuƙa Watanni Biyu Bayan Aurensu A Kano
Wani mutum mai shekaru 45, Auwalu Adamu, ya rasa ransa bayan da ake zargin sabuwar matarsa ta biyu, Khadija Sulaiman, ta daba masa wuƙa har lahira, watanni biyu kacal bayan ɗaurin aurensu a unguwar Hayin Lawali da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a Jihar Kano.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi bayan wata sa-in-sa mai zafi da ta ɓarke tsakanin ma’auratan a gidansu.
Farashin Fetur Na Iya Sauka Zuwa Naira 900 Kan Kowace Lita —Masana
Mazauna yankin sun bayyana cewa tun farkon aurensu ake fama da rashin jituwar da ke tsakaninsu, inda sabanin ya kan rikide zuwa rikice-rikicen da jama’a ke gani a fili.
Wani maƙwabcin mamacin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce Auwalu ya fito daga gidansa cikin jini bayan ya samu mummunan rauni a wuya sakamakon sara da wuƙa.
“Ya fito daga gidan yana zubar da jini. Da alama ya yi ƙoƙarin dakatar da zubar jinin da wani yadi, amma kafin mu kai gare shi ya durƙushe kuma ya kasa magana. Daga bisani ya rasu a wurin,” in ji maƙwabcin.
Wani mazaunin yankin ya ce yawan saɓani da rikicin da ke tsakanin ma’auratan ya kasance abin damuwa ga al’ummar yankin tun bayan aurensu.
Shugaban wata ƙungiyar tsaron al’umma a yankin, Nazifi Abdullahi, ya ce bayan aukuwar lamarin matar ta yi yunƙurin tserewa, amma wasu mata maƙwabta sun cafke ta tare da riƙe ta har zuwa lokacin da jami’an ’yan sanda suka isa wurin.
“Ba su kai watanni biyu da yin aure ba, kuma ita ce matarsa ta biyu. Kwatsam sai muka ji ya fito daga gida da raunin wuƙa a jikinsa sannan ya faɗi ƙasa. Ana zargin matar ce ta daba masa wuƙar. Ta yi ƙoƙarin tserewa amma mata maƙwabta suka hana ta guduwa har sai da ’yan sanda suka zo,” in ji Abdullahi.
Zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan lamarin ba.
-
News5 days ago
ICPC Ta Yi Barazanar Daurin Shekaru 7 Ga Masu Yiwa Baki Rajistar NIN A Matsayin Yan Najeriya
-
News1 day ago
Jam’iyyar ADC Ta Yi Watsi Da Cire Ta Daga Rijista, Ta Sha Alwashin Kalubalantar Hukuncin Kotu
-
News6 days ago
Hayar Jirage Hadi Sirika Ya Dakko Daga Habasha Don Damfarar Yan Najeriya Da Sunan “Nigeria Air” — Shaida
