News
Jami’an NDLEA Sun Cafke Tsofaffi Biyu Kan Zargin Sayar Wa Ɗaliban Sakandare Miyagun Ƙwayoyi
Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kama wasu dattawa biyu masu shekaru 84 da 75 a birnin Umuahia na Jihar Abiya bisa zargin sayar da miyagun ƙwayoyi ga ɗaliban makarantun sakandare.
Waɗanda aka kama sun haɗa da Godfrey Orji da Godwin Obulunbiya Obiora, bayan samun bayanan sirri kan ayyukansu.
Manchester United Ta Mallaki Filin Gina Sabon Filin Wasa Mai Daukar Mutane Dubu Dari
Jami’an NDLEA sun kama Obiora ne a ranar 19 ga Yuni, 2026, a wani shagon sayar da magunguna da yake gudanarwa a kan titin Club Road da ke Umuahia.
A binciken da aka yi a shagon, an gano kilogram 4.64 na miyagun ƙwayoyi, ciki har da tramadol da diazepam, waɗanda ake zargin yana sayarwa ga matasa da sauran masu amfani.
Shi kuwa Orji, wanda tsohon ma’aikaci ne mai ritaya, jami’an tsaron makarantar Saint Silas Secondary School da ke Old Umuahia ne suka kama shi yayin da ake zarginsa da bai wa wasu ɗalibai biyu miyagun ƙwayoyi. Daga bisani aka miƙa shi ga ‘yan sanda, waɗanda suka tura shi hannun NDLEA domin ci gaba da bincike.
Wani ɗalibi mai shekara 15 da ke aji na SS2 ya shaida wa masu bincike cewa Orji ne ke ba shi ƙwayoyin da yake amfani da su tare da sake sayar wa wasu abokan karatunsa.
Hukumar ta ce za ta gurfanar da dattawan biyu a gaban kotu, yayin da aka tura ɗaliban da abin ya shafa domin samun kulawar gyaran hali da shawarwari.
A wani samame da ta gudanar a Legas, NDLEA ta kama wani kaya mai ɗauke da kilogram 9.5 na sinadarin ADB Chminaca, wani sabon nau’in ƙwaya mai haɗari da aka shigo da shi daga ƙasar China. Haka kuma, jami’an sun gano gram 300 na tabar wiwi mai ƙarfi da aka ɓoye cikin jakunkunan mata a wani kamfanin jigilar kaya.
Har ila yau, hukumar ta kama wasu da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi a jihohin Legas, Kogi da Ekiti, ciki har da wasu ma’aurata da ake nema ruwa a jallo tun bayan kama kilogram 117 na tabar wiwi a watan Maris. A Jihar Kogi kuma, an kama wani mutum ɗauke da methamphetamine da aka ɓoye cikin kwalayen custard yayin tafiyarsa daga Legas zuwa Abuja.
