Connect with us

News

CBN: Umarnin Akanta Janar Ya Sa Muka Buɗe Wa PFIPC Asusu

Published

on

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa buɗe asusun Hukumar PFIPC ya biyo bayan umarnin da Ofishin Akanta Janar na Tarayya ya bayar, ba tare da bankin ya yi hakan da kansa ba.

Wannan bayani ya fito ne ta bakin wani babban darakta a CBN, Hamisu Abdullahi, yayin da yake wakiltar Gwamnan Babban Bankin a gaban Kwamitin Majalisar Wakilai da ke binciken sahihancin kafuwar hukumar PFIPC.

DSS Za Ta Ɗaukaka Ƙara Kan Hukuncin Ɗaurin Rai Da Rai Da Aka Yanke Wa Shugabannin Ansaru

A cewarsa, shugaban hukumar ya gabatar da takardun da suka nuna cewa Ofishin Akanta Janar na Tarayya ne ya bayar da umarnin buɗe asusun hukumar a ranar 30 ga Yulin 2025.

Kwamitin Majalisar Wakilan na gudanar da bincike kan sahihancin kafa PFIPC, yadda take gudanar da ayyukanta, da kuma yadda aka saka kasafin kuɗinta cikin kasafin gwamnatin tarayya, duk da zarge-zargen cewa ba a kafa hukumar bisa tanadin doka ba.

A wani ɓangare kuma, Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa (ICPC) ta gayyaci Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila, domin yi masa tambayoyi kan wasu zarge-zargen da mutumin da ke ikirarin shi ne Darakta Janar na PFIPC, Prince Adeniyi Adeyemi, ya yi.

Advertisement

Adeyemi ya yi zargin cewa ya biya Naira miliyan 400 domin samun muƙamin Darakta Janar, sannan ya ce an nemi kaso 48 cikin 100 na kuɗin fara aikin hukumar, wanda ya kai Naira biliyan 27.3.

Sai dai Gbajabiamila ya musanta waɗannan zarge-zarge, tare da shigar da ƙarar ɓata suna a kotu, inda yake neman a biya shi diyyar Naira biliyan 15.

Rahotanni sun kuma nuna cewa an ware fiye da Naira biliyan 1.3 ga PFIPC a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026, lamarin da ya ƙara jawo tambayoyi kan yadda aka saka sunan hukumar cikin kasafin kuɗin ƙasa.

Binciken ya kuma nuna cewa Adeyemi ya samu amincewar ɗaukar ma’aikata 300 aiki, tare da samar wa hukumar ofis a Sakatariyar Gwamnatin Tarayya da ke Abuja, sannan aka buɗe mata asusu a CBN.

Sai dai Babban Bankin ya bayyana cewa asusun biyu da aka buɗe wa hukumar ba su fara aiki ba, saboda har yanzu ba a gabatar da sunayen mutanen da aka ba izinin sa hannu wajen gudanar da su ba.

Ana sa ran binciken da Majalisar Wakilai ke yi zai fayyace sahihancin kafuwar PFIPC, tare da gano yadda aka saka hukumar cikin tsarin kasafin kuɗin gwamnatin tarayya.

Advertisement

 

RFI

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending