Connect with us

News

Ana Fargabar Dalibai Sun Maƙale Bayan Rushewar Ginin Dakunan Kwana Mai Ɗakuna 90 A Anambra

Published

on

IMG 20260727 170455 006

Ana ci gaba da aikin ceto bayan da wani ginin dakunan kwanan ɗalibai mai hawa uku ya rushe a garin Oko da ke Ƙaramar Hukumar Orumba ta Arewa a Jihar Anambra, inda ake fargabar cewa ɗalibai da dama sun maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzan ginin.

Rahotanni sun ce ginin mai suna Elite Five Star Lodge, wanda ke da sama da ɗakuna 90, ya rufta ne a daren Lahadi a unguwar Amokpala, kusa da Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Tarayya da ke Oko.

Ruwan Sama Mai Karfi Ya Rusa Gidaje Sama Da 300 A Katsina

Bayan aukuwar lamarin, mazauna yankin da ɗalibai sun yi gaggawar kai ɗauki, yayin da aka rika jin kukan neman ceto daga ƙarƙashin ginin.

Jami’an hukumar ba da agajin gaggawa, rundunar ‘yan sanda, hukumar kashe gobara da sauran jami’an tsaro sun isa wurin domin gudanar da aikin ceto.

An ceto wasu daga cikin waɗanda suka ji raunuka, kuma an garzaya da su asibiti domin samun kulawar likitoci. Sai dai ana ci gaba da neman wasu da ake kyautata zaton har yanzu suna ƙarƙashin ɓaraguzan ginin.

Advertisement

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa jami’an tsaro sun killace wurin domin bai wa masu aikin ceto damar gudanar da aikinsu cikin sauƙi.

Ya kuma bukaci al’umma su kwantar da hankalinsu, su guji yaɗa jita-jita, tare da kauce wa wurin domin kada su hana masu aikin ceto gudanar da aikinsu.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, hukumomi ba su bayyana adadin waɗanda suka mutu ko waɗanda har yanzu suke maƙale ba, yayin da ake ci gaba da aikin ceto.

 

 

TRT AFRIKA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending