Connect with us

News

Haɗin Gwiwar Gwamnatin Kano Da Ƙungiyoyin Fararen Hula Zai Taimaka Wajen Wayar da Kan Al’umma Kan Ayyukan Gwamnati – Bilkisu Indabo

Published

on

IMG 20260806 162601 666

Mai Bai wa Gwamnan Jihar Kano Shawara ta Musamman kan Harkokin Wayar da Kai, Hajiya Bilkisu Yakubu Indabo, ta bayyana cewa shirin Government–NGO Handshake zai taimaka matuƙa wajen wayar da kan al’umma game da manufofi da ayyukan ci gaba da Gwamnatin Jihar Kano ke aiwatarwa.

Ta ce shirin, wanda gwamnati ke shirin ƙaddamarwa, zai samar da ingantacciyar haɗin gwiwa tsakanin hukumomin gwamnati da ƙungiyoyin fararen hula domin bunƙasa wayar da kan jama’a, ƙarfafa gaskiya da riƙon amana, tare da ƙara wa al’umma damar shiga cikin harkokin ci gaban jihar.

Gwamna Abba Ya Samu Kyautar WINSEC, Waiya Ya Lashe Lambar Yabo Kan Dabarun Sadarwa

A cewarta, ƙungiyoyin fararen hula za su kasance abokan hulɗa na gwamnati wajen wayar da kan jama’a, gudanar da shirye-shiryen faɗakarwa, tattara ra’ayoyin al’umma da kuma tabbatar da cewa bayanai kan ayyukan gwamnati sun isa ga kowane sashe na al’umma, musamman mata, matasa, masu buƙata ta musamman da sauran rukunin da ke da rauni.

Hajiya Bilkisu Indabo ta bayyana cewa shirin zai ƙarfafa sadarwa tsakanin gwamnati da al’umma, ta yadda jama’a za su fi fahimtar manufofi da shirye-shiryen raya ƙasa da gwamnatin jihar ke aiwatarwa.

Ta ce samar da sahihan bayanai cikin lokaci zai ƙara inganta gaskiya da riƙon amana, tare da ƙarfafa amincewar jama’a ga gwamnati da ayyukanta.

Advertisement

Baya ga hakan, ta ce shirin zai ƙarfafa al’umma su shiga cikin tsarawa, aiwatarwa da kuma sanya ido kan ayyukan ci gaba, lamarin da zai taimaka wajen inganta aiwatar da ayyuka da tabbatar da cewa sun dace da buƙatun al’umma.

Ta ƙara da cewa za a samar da tsari na musamman na tattara ra’ayoyi da ƙorafe-ƙorafen jama’a, wanda zai taimaka wa hukumomin gwamnati wajen gano ƙalubalen da ke tattare da aiwatar da ayyuka da kuma inganta manufofi da shirye-shiryenta bisa bayanan da aka samu daga al’umma.

A cewar ta, haɗin gwiwar tsakanin gwamnati da ƙungiyoyin fararen hula zai ƙara inganta wayar da kan jama’a, faɗaɗa shigar al’umma cikin harkokin mulki da kuma tabbatar da cewa ayyukan raya ƙasa suna haifar da sauyi mai ma’ana ga al’ummomin Jihar Kano.

Hajiya Bilkisu Indabo ta bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a sanar da ranar ƙaddamar da shirin Government–NGO Handshake, wanda ake sa ran zai zama wani muhimmin mataki na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Jihar Kano da ƙungiyoyin fararen hula domin cimma ci gaba mai ɗorewa.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending