News
“Daga Ranar Da Aka Zaɓe Ni Zan Soke Dokar Fanshon Gwamnoni A Kano” — Ibrahim Little Ɗan Takarar Gwamna A Jam’iyyar ADC
Ɗan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), Alhaji Ibrahim Ali Amin Little, ya bayyana cewa zai soke dokar da ta bai wa tsofaffin gwamnoni damar karɓar fansho da wasu alawus-alawus, idan aka zaɓe shi a matsayin gwamnan jihar a 2027.
Little ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a Kano, yayin wani taron manema labarai, inda ya kuma sanar da zaɓen Abdulkadir Shehu Bari daga Ƙaramar Hukumar Rogo a matsayin abokin takararsa na mataimakin gwamna.
Ibrahim Ali Amin Little Ya Zaɓi Abdulkadir Shehu Bari A Matsayin Abokin Takararsa A 2027
Ya ce daga ranar da aka zaɓe shi kuma ya hau kujerar gwamna, zai ɗauki matakin sake duba dokokin da suka shafi biyan tsofaffin gwamnoni fansho, yana mai cewa ana amfani da tsarin wajen karkatar da dukiyar jama’a.
«“Daga ranar da aka zaɓe ni zan cire dokar da ta ba da damar ba gwamnoni fansho, domin ana amfani da shi wajen sace kuɗaɗen al’ummar Kano,” in ji Little.»
Ɗan takarar ya ce gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen tabbatar da cewa kuɗaɗen jihar sun fi karkata ne zuwa ayyukan da za su inganta rayuwar al’umma, musamman a fannonin ilimi, kiwon lafiya, samar da ayyukan yi da ƙarfafa matasa da mata.
Ya kuma yi alkawarin magance matsalolin da suka addabi fannin ilimi da lafiya, tare da samar da shirye-shiryen tallafa wa marasa galihu, musamman zawarawa, marayu da yaran da ba sa zuwa makaranta.
Little ya ce gwamnatinsa za ta ƙarfafa harkokin kasuwanci da ƙirƙire-ƙirƙire ta hanyar samar da cibiyoyin sana’o’i da kasuwanci a sassa daban-daban na jihar.
A cewarsa, shirin zai taimaka wajen sauya Kano daga al’umma mai yawan dogaro da shigo da kayayyaki zuwa jihar da ke samarwa, samar da ayyukan yi da kuma ƙirƙirar arziki.
Ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta yi aiki da tsarin mulkin kowa da kowa, tare da bai wa ‘yan ƙasa damar shiga cikin harkokin ci gaban jihar ba tare da la’akari da matsayinsu ko asalinsu ba.
Little ya yi kira ga al’ummar Kano da su bai wa jam’iyyar ADC goyon baya a zaɓen 2027, yana mai cewa manufofinsa sun mayar da hankali ne kan inganta rayuwar jama’a da kuma tabbatar da amfani da dukiyar jihar wajen amfanin al’umma.
