Connect with us

News

Kwamishinan Yaɗa Labaran Kano, Waiya Ya Samu Lambar Yabo Ta Ƙasa Kan Ƙwarewar Yaɗa Labarai A Lokutan Rikici ‎

Published

on

1786649468928

‎Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kano, Comrade Ibrahim Abdullahi Waiya, ya samu lambar yabo ta ƙasa kan ƙwarewar sadarwa a lokacin rikici.

‎An karrama kwamishinan da lambar Outstanding Crisis Communicator Award ne a bikin bayar da lambobin yabo na National Spokespersons Awards 2026, wanda aka gudanar a Nicon Luxury Hotel da ke Abuja ranar Alhamis.

Wasu ’Yan Fashi Sun Shafe Awanni Shida Suna Cin Abinci A Gidan Da Suka Je Sata

‎An bayyana cewa an ba Waiya lambar yabon ne saboda rawar da yake takawa wajen sadarwa da jama’a a lokacin rikice-rikice, tare da tabbatar da isar da sahihan bayanai kan manufofi, shirye-shirye da ayyukan Gwamnatin Jihar Kano.

‎Shugaban Image Merchants Promotions Limited (IMPR), Farfesa Sule Ya’u Sule, wanda ke cikin masu shirya bikin, ya ce an zaɓi Waiya ne bayan an yi la’akari da irin ƙoƙarin da yake yi wajen samar da sahihin bayani cikin lokaci da kuma tafiyar da harkokin sadarwa a lokacin da ake fuskantar matsaloli da damuwar jama’a.

‎Ya ce karramawar ta nuna muhimmancin ingantacciyar sadarwa wajen ƙarfafa fahimtar juna tsakanin gwamnati da jama’a, da kuma gina amincewar jama’a ga manufofi da shirye-shiryen gwamnati.

Advertisement

‎Da yake karɓar lambar yabon, Waiya ya gode wa masu shirya taron bisa karrama shi, yana mai cewa lambar za ta ƙara masa ƙwarin gwiwar ci gaba da aikinsa na samar da bayanai masu inganci ga al’umma.

‎Kwamishinan ya sadaukar da lambar yabon ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da ma’aikatan Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, da kuma kafafen yaɗa labarai na jihar bisa goyon baya da haɗin gwiwar da suke bayarwa.

‎Ya ce isar da sahihin bayani cikin lokaci na da matuƙar muhimmanci wajen kyakkyawan shugabanci, musamman a lokacin da ake fuskantar rikici ko rashin tabbas.

‎Waiya ya ƙara da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da ƙoƙarin tabbatar da cewa al’ummar Jihar Kano na samun sahihan bayanai kan manufofi, shirye-shirye da ayyukan gwamnati cikin lokaci.

‎Ya jaddada cewa ingantacciyar sadarwa a lokacin rikici na buƙatar ƙwarewa, gaskiya, da fahimtar abubuwan da ke damun jama’a.

‎A bikin, tawagar Jihar Kano ta haɗa da Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai na Majalisar Dokokin Jihar Kano, Hon. Sa’ad Aminu Ungogo, da Hon. Salisu Riruwai, mamba a kwamitin.

Advertisement

‎Haka kuma, jami’ai da ma’aikatan Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, shugabannin hukumomin ma’aikatar da wakilan ƙungiyoyin ƙwararrun kafafen yaɗa labarai, ciki har da NUJ, NAWOJ, NGE, NIPR da Society of Nigerian Broadcasters, sun halarci bikin.

‎Sauran waɗanda suka halarta sun haɗa da League of Veteran Journalists, wakilan Online Media Chapel, masana harkokin sadarwa, jami’an yaɗa labarai na ƙananan hukumomi, abokai da ’yan uwa.

‎Karramawar ta ƙara jaddada muhimmancin rawar da ƙwararrun masu magana da yawun gwamnati ke takawa wajen samar da fahimtar juna da amincewa tsakanin gwamnati da jama’a.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending