News
A Shirye Nake Na Fuskanci Cikakken Bincike Kan Zargin Alaƙa Da ’Yan Bindiga — Sanata Shehu Buba
Sanatan Bauchi ta Kudu, Shehu Buba Umar, ya ce a shirye yake ya fuskanci cikakken bincike daga hukumomin tsaro kan zarge-zargen da ake yi masa na alaƙa da ’yan bindiga, ɗaukar nauyin ta’addanci ko garkuwa da mutane.
Sanatan ya ce har ma da kansa ya miƙa kansa ga Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) domin gudanar da bincike kan zarge-zargen, yana mai cewa ba shi da wani abin da yake ɓoyewa.
Zanga-zanga Ta Barke Kan Karin Kudin Man Fetur A Syria
Da yake magana da ’yan jarida a Bauchi ranar Litinin, Shehu Buba ya ce, “Babu abin da nake ɓoyewa, kuma babu wani abin da nake fargabar a bankaɗo a kaina.” Ya musanta zarge-zargen gaba ɗaya, yana mai cewa bai taɓa ɗaukar nauyin ’yan bindiga ko tallafa musu da kuɗi, makamai ko wata hanya ba.
Sanatan ya ce zarge-zargen sun fara ne tun shekarar 2024 a matsayin wani salo na yaƙin siyasa, kafin daga bisani su sake bayyana ta wasu hanyoyi.
Ya bayyana cewa tawagar lauyoyinsa ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA), Yakubu Chonoko Maikyau, SAN, ta rubuta wa DSS, Hukumar Leƙen Asirin Tsaro ta Sojoji (DIA) da Rundunar ’Yan Sanda, inda ta nemi hukumomin su gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen.
Buba ya ƙalubalanci duk wanda yake da hujjar alaƙarsa da ’yan bindiga, ta’addanci ko garkuwa da mutane da ya miƙa hujjojin ga hukumomin tsaro maimakon ya yaɗa zarge-zargen a kafafen sada zumunta.
Ya ce a shirye yake a gurfanar da shi a gaban kotu tare da fuskantar hukunci idan bincike ya tabbatar da cewa yana da hannu a cikin laifukan da ake zarginsa da aikatawa.
Sanatan ya kuma buƙaci hukumomin tsaro su gayyaci mutanen da ke yaɗa zarge-zargen domin su gabatar da hujjojin da suke da su.
Buba ya ƙara da cewa a lokacin da yake jagorantar Kwamitin Majalisar Dattawa kan Tsaron Ƙasa da Leƙen Asiri, ya yi aiki tare da sojoji da hukumomin leƙen asiri wajen yaƙi da ’yan bindiga, ta’addanci da garkuwa da mutane.
Ya kuma ce lauyoyinsa sun gano wani mutum mai suna Hassan Saleh Hussaini, wanda ya zarge shi da hannu wajen yaɗa wasu daga cikin zarge-zargen daga Jamhuriyar Nijar.
A cewarsa, an kai rahoton lamarin ga hukumomin da suka dace domin neman taimakon Interpol, yayin da aka ɗauki lauyoyi a Nijar domin bin hanyoyin shari’a.
Shehu Buba, wanda yake ɗan takarar gwamnan Jihar Bauchi na jam’iyyar PRP a zaɓen 2027, ya ce yana ganin wasu na amfani da zarge-zargen a matsayin yaƙin siyasa domin rage masa damar samun nasara a zaɓen.
