Connect with us

News

Mun kashe ‘yan bindiga 30 bayan harin da suka kai mana a Abuja – Sojin Najeriya

Published

on

Sojin Najeriya

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Aƙalla ‘yan bindiga da gwamnatin Najeriya ke kira ‘yan ta’adda 30 ne jami’an tsaro suka kashe a Abuja babban birnin ƙasar bayan sun kai hari kan rundunar tsaro ta fadar shugaban ƙasa, a cewar rundunar sojan ƙasar.

 

Advertisement

A ranar Talata ne wasu ‘yan bindiga suka yi wa sojojin kwanton-ɓauna, inda kashe uku daga cikinsu tare da raunata wasu da dama lokacin da suke barin makarantar horon lauyoyi da ke yankin Bwari.

An shigar da ƙarar Yarima Mohammed Bin Salman na Saudiyya a Faransa

Advertisement

Da yake magana yayin wani taron manema labarai ranar Alhamis, shugaban sashen hulɗa da jama’a na rundunar, Manjo Janar Bernard Onyeuko, ya ce dakarun Bataliya ta 7 ne da Dakarun Musamman na 167 suka ƙaddamar da samamen tsakanin Lahadi zuwa Talata.

 

Advertisement

Ya ƙara da cewa dakarun sun yi nasarar kashe ‘yan bindigar a ƙauyukan Kawu da Ido ta hanyar tarwatsa sansanoninsu.

 

Advertisement

A cewarsa, dakarun sun ƙwato babur shida, da bindigar AK-47 biyu da sauransu a yayin samamen

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending