Connect with us

Sports

Haaland ya fara biyan kudin sabulu a Manchester City

Published

on

Daga Muhammad Muhammad zahraddin

Manchester City ta fara kakar bana da kafar dama, bayan da ta je ta doke West Ham United a gasar Premier League da ci 2-0 ranar Lahadi.

Advertisement

Sabon dan wasan da City ta dauko a bana Erling Haaland, shi ne ya ci mata kwallon farko a bugun fenariti, kuma shi ne dai ya kara na biyu a raga.

‘Yan wasan West Ham

Advertisement
West Ham

Indaranka

Wannan shi ne karo na hudu da suka hadu a wasan fara gasar Premier League, inda West ta yi rashin nasara a fafatawa uku baya.

Kuma a wasa 14 da suka kara baya, City ta yi nasara a 10 da canjaras uku, ciki har da 2-2 da suka tashi a gidan West Ham a Premier League ranar 15 ga watan Mayu.

West Ham tana rike da tarihin wadda ke kasa cin wasa karo na14 a duk ranar bude gasar Premier League, wato wasanta na farko, tun kan karawa da City ranar Lahadi.

Advertisement

Haaland ya ci kwallo uku rigis a wasan farko a Champions League da ya buga wa Red Bull Salszburg.

Haka kuma ya zura uku rigis a karon farko da ya fara Bundesliga a Borussia Dortmund.

Advertisement

‘Yan wasan Manchester City

Man City

Indaranka

Advertisements
Advertisements

Manchester City ita ce mai rike da Premier League biyu a jere, wadda ta dauki na kakar da ta wuce da tazarar maki daya tsakaninta da Liverpool a ranar karshe.

City ta ci wasa 29 a bara da canjaras shida, sannan ta yi rashin nasara a fafatawa uku a kakar da aka kammala.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending