News
ASUU ta garzaya kotun ɗaukaka ƙara
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADEEN
Kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, ta garzaya kotun ɗaukaka kara da ke zamanta a Abuja, inda ta bukaci ta yi watsi da hukuncin da kotun masana’antu ta kasa, NIC, ta yanke na janye yajin aikin da ta shafe watanni bakwai tana yi.
Kungiyar, a cikin ƙorafe-ƙorafe 14 da ta shigar, ƙarƙashin tawagar lauyoyinta karkashin jagorancin wani dan rajin kare hakkin bil’adama, Femi Falana, SAN, ta kuma bukaci a dakatar da aiwatar da hukuncin.
Taliban zata Haramta amfani da Tiktok Sabida Yana Assasa tashin Hankali
Idan dai ba a manta ba, a hukuncin da NIC ta yanke a ranar Larabar da ta gabata ta hannun mai shari’a Polycarp Hamman, ta umurci malaman jami’o’in da ke yajin aikin da su koma ajujuwa, har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan karar da gwamnatin tarayya ta shigar domin neman sahihancin yajin aikin na su.
Dokar wucin gadi ta umurci mambobin ASUU da su koma bakin aiki, ya biyo bayan bukatar da FG ta shigar ta hannun lauyanta, Mista James Igwe.
