News
A Baya ta Mallaki Motoci da Gidaje: Amma Yanzu Ta Talauce Tana Bara a Titi
DAGA KHADIJA ABDULLAH MUHMD
Wata Mata mai suna Dorcas Kagendo wacce ta kasance Milinoya mai kudi amma daga baya aka ganta a titi tana bara.
Dorcas ta zama Miloniya tun tana yar shekara 33 kuma ta mallaki motoci da gida kafin iftila’i ya fada mata shekaru biyu da suka gabata.
Bayan talaucewar da tayi, yanzu tana fama da cututtuka daban-daban Tana gab da hallaka rayuwarta.
Za mu mutunta sojojin Russia idan su ka miƙa wuya — Zelensky
Dorcas Kagendo, wata ‘yar shekar 50 wacce ta kasance attajira tana kira ga jama’a su kawo mata dauki.
Matar yar kasar Kenya ta kasance mai kudi lokacin tana matashiya amma abubuwa suka sauya daga baya.
Tashar Afrimax ta yi hira da Dorcas wacce aka gani a titi tana bara.
Ta ce bayan kammala karatu, ta samu aikin sakatare daga baya kuma ta zama jagora.
Daga nan ta fara samun kudi inda ta sayi manyan motoci, gidaje da kadarori. Hakazalika tayi aure amma Mijin ya tafi daga baya.
An nuna hotunan motocin da ta siya lokacin da take cin gari.
Dorcas tace rayuwarta ta fara samun matsala ne lokacin da ta samu wani aiki a kasar Saudiyya.
Ba da dadewa ba ta fara fama da ciwon koda, ciwon siga, ciwon hunhu, da kansa. Sakamakon haka aka koreta daga Saudiyya.
Tace ta koma gida Kenya inda ta fara sayar da dukiyoyinta don jinya, har komai ya kare.
