News
Lalata ’Yar Makwabci Ya Sa Kotu Tsare Dan Acaba
DAGA YASIR SANI ABDULLAH
Kotun Majistare da ke Ikeja a Jihar Legas ta tsare wani mai sana’ar acaba mai shekara 33 da ya yi fyade ga ’yar makwabcinsa.
Alkaln kotun, Misis B.O. Osunsanmi, a bayar da umanin ne bayan an gurfanar da matashin a gabanta ranar Alhamis kan zargin aikata fyade.
Galatasaray na zawarcin Ronaldo, Kante na fuskantar rashin tabbas a Chelsea
Dan sanda mai gabatar da kara ya shaida wa kotun cewa a ranar 2 ga watan Satumba ne wanda ake zargin a zakke wa karamar yarinyar mai shekara 10 a gidansa da ke unguwar Ikorodu.
Bayan umarnin tsare dan acaban, kotun ta bayar da umarnin a mika fayil din kes dinsa zuwa ofishin gurfanar damasu laifi na gwamnatin jihar.
Daga nan ta daage sauraron shari’ar zuwa ranar 27 ga watan Oktoba da muke ciki.
AMINIYA
