News
INEC ta saka ranar gudanar da zaɓuka a jihohin Bayelsa, da Imo, da Kogi
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya ta tsayar da ranar 11 ga watan Nuwamban 2023, domin gudanar da zabukan gwamna a jihohin Bayelsa, da Imo da kuma jihar Kogi
Babban kwamishina a hukumar, kuma shugaban kwamitin bayar da bayanai da ilimantarwa na hukumar zaɓen Festus Okoye ne ya bayyana haka ranar Talata a Abuja babban birnin kasar.
NDLEA ta kama mutum 192 da ake zargi da safarar kwaya
Ya ce hukumar zaɓen ta cimma wannan matsaya ne a taronta na mako-mako da ta gudanar ranar Talata.
Mista Okoye ya ƙara da cewa za a gudanar da zaɓukan fitar da gwani a jihohin uku daga ranar 27 ga watan Maris zuwa ranar 17 ga watan Afrilun 2023.
Advertisements
