News
shekara guda da wallafa fassarar littafin muwadda malik zuwa harshen hausa da DR AHMED IBRAHIM BAMBA( B U K) yayi
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
A yau 7 ga watan nuwanbar shekarar 2022 rana ce da fitaccen malamin addinin musulunci nan a nigeria margayi Dr Ahmad Ibrahim Bamba ( b u k) ya shekara Daya 1 da fassara littafin muwadda Malik zuwa harshen Hausa.
Marigayi b u k ya wallafa fassarar muwadda Malik ne a ranar 7 ga watan nuwambar shekarar 2021 Kuma ya wallafa littafin a watanni biyu kafin rasuwar sa.
Hukumar NiMet Ta Yi Hasashen Samun Kwalleliyar Rana na Kwanaki Uku
A Wata tattaunawa da jaridar indaranka tayi da Wani daga cikin yayan marigayi malam ya,ce mahaifin su ya dauki tsawan lokaci Yana wannan aiki na fassara wannan babban littafin musulunci
Dr Bamba ya kaddamar da fassarar littafin ne a cikin makarantar Jami,ar bayero university sabuwa wacce ake kira da ( new site) Kuma Baki daga ko Ina a fadin kasar nar sun samu halartar zuwa wajan wallafa littafan.
Cikin wadanda suka halarci Taron kaddamar da littafin sun Hadar da ministan sadarwa da tattalin arziki na kasa Dr Ali Ibrahim fantami da shugaban kamfanin Mai na kasa mele kyari.
Sai Kuma manyan malaman addinin musulunci da suka hada da bangarori daban daban da Kuma Yan siyasa da Kuma manyan masu arzuki na kasa ba ki daya.
Dr Ahmad Bamba ya kasan,ce tsohon malami a Jami,a a fannin nazarin koyar da harshen larabci da hadisi a Jami,ar bayero university kano
Yau watanni 10 chif da rasuwar marigayi Dr Ahmad Ibrahim Bamba
Malamin ya rasu a ranar juma,a 7 ga watan jumairun shekarar 2022 Kuma ya mutu ya bar Yaya da mata da jikoki
