News
Somaliya ta haramta amfani da kalmar ‘al-Shabab’ kan kungiyar ‘yan ta’adda
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Hukumar da ke kula da al’amuran addini ta Somaliya ta haramta amfani da kalmar al-Shabab – wadda a harshen Larabci ke nufin ‘Matasa’ – kan kungiyar ‘yan ta’addan kasar.
Hukumar ta yi kira ga al’umar kasar da su kira kungiyar da sunan “Khawarij” wato wadanda suka yi tawaye.
Gwamnatin kasar ta ce umarnin kiran al-Shabab da “Khawarij” na daga cikin manufofinta na yaki da kungiyar.
Wannan dai ba shi ne karo na farko da Somaliya ke sanya wa al-Shabab wani suna ba.
A shekarar 2015 ma gwamnatin kasar ta shaida wa kafofin yada labarai da su rika kiran kungiyar da suna ‘Ugus” wata inkiya da ‘yan kasar ke yi wa ‘kungiyar da ta yi wa ‘yan kasar kisan kiyashi”.
A martanin da ta mayar, kungiyar ta yi gargadin hukunta duk wanda ya bi umarnin gwamnatin cikin har da ‘yan jarida wajen kiranta da sabon sunan.
A watan da ya gabata, hukumomin kasar suka haramta wa kafofin yada labaran kasar yin labaran da suka shafi ayyukan kungiyar.
