Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Sace Kananan Yara 20 A Neja

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

’Yan bindiga sun yi garkuwa da kananan yara 20 masu shekaru hudu zuwa 10 a garin Kusherki da ke Karamar Hukumar Rafi ta Jihar Neja.

 

Advertisement

16 daga cikin kananan yaran da ’yan ta’addan suka sace mata ne kuma a halin yanzu sun yi sayi uku a hannun masu garkuwa da su.

 

Advertisement

Chelsea ta dage kan Endrick, Utd na son Diaz, Depay zai tafi, Klopp na nadama

Mazauna garin sun ce masu garkuwa da yaran na neman Naira miliyan 40 a matsayin kudin fansa kuma suna azabtar da yaran.

Advertisement

 

Aminiya ta rawaoto cewa Iyayen yaran sun yi kira ga gwamnati da ta kawo musu dauki wajen kubutar da ’ya’yan nasu.

Advertisement

 

Mazauna yankin sun bayyana cewa a ’yan makonnin nan ’yan bindiga sun dawo da cin karensu babu babbaka a yankunan Rafi da Magama da kuma hanyar Zungeru zuwa Tegina.

Advertisement

 

Hakan, a cewarsu ya jefa zullumi a zukatan wadanda suka fara girbe amfanin gonarsu.

Advertisement

 

Wani mazaunin yankin mai suna Abdullahi Ibrahim ya ce har yanzu akwai ’yan uwansu da aka yi garkuwa da wata hudu da suka gabata a hannun ’yan bindiga.

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending