News
Kudurori Na 5 Masu Kyau Ne Ga Karamar Hukumar Dala – Bandirawo
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Dan takarar Majalisar jaha a Karamar Hukumar Dala a jam, iyyar Action Democratic party (ADP) Honorable Usman Sagiru Bandirawo ya gabatar da kudurorin sa guda 5 wanda ya kuduri aniyar yi, idan aka zabe shi a matsayin dan Majalisar jaha mai wakiltar Dala.
Ya gabatar da Kudurorin nasa ne yayin tataunawa da wakilan jaridar indaranka Yasir sani Abdullahi
Dan takarar gwamnan jihar Kano a ADP ya taya malam Ibrahim shakarau murnar ranar haihuwar sa @67
Cikin manufofin da na kudira sun Hadar da Ilimi, Lafiya, Ruwan Sha, samawa matasa aikin yi, da kuma tsaro
Bandirawo yace yanada gogewa wajen kawar da dukkan wadannan matsalolin da gaugawa dake addabar mutanen yankin
Dan Takarar karamar Hukumar Dala jam, iyyar ADP, ya kuma sha Alwashin kyutata mu,amala tsakanin,sa da Al, ummmar sa dan tabbatar da sahihin Mulki
Haka kuma ya ce bazai yi watsi da fannin boko da Ilimin Addini ba, a matakan Firamare da Sikandire da kuma gaba da Sikandire.
Ya,ce karamar hukumar Dala tana San mutum jajirtacce Kuma matashi irina Wanda yayi gogwarmaya yasan irin matsalolin da ke zama matsalolin ga yankin
Kazalika, ya sake Jaddada kudurin sa na kare Muhalli, ta hanyar kirkirar Shirye-shiryen hana saran Daji da Shuka bishiyoyi da kuma bunkasa fannin Albarkatun kasa
