News
Sudan na iya darewa’~Abdelaziz al-Hilu
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Wani jagoran kungiyar ƴan haƙoro masu ɗauke da makami a Sudan ya ce akwai haɗarin cewar ƙasar za ta iya darewa kasancewar jagororin mulkin sojin ƙasar na yanzu ba su da niyyar bin hanyoyin diflomasiyya wajen samar da zaman lafiya.
Shugaban ƙungiyar ta Sudan Peoples Liberation Army (SPLA-North), Abdelaziz al-Hilu ya faɗa wa BBC cewa ƙungiyarsa za ta nemi darewa daga ƙasar matuƙar gwamnatin Sudan ba ta sauya yadda take tafiyar da al’amuranta ba.
Kotu ta umarci A.A Zaura ya gurfana a gabanta kan zargin rashawa
Ƙungiyar SPLA-North tana iko da yanki mai girma na tuddan Nuba da ke kudancin ƙasar, da kuma yankin Blue Nile.
Mr al-Hilu ya ce ƙungiyarsa za ta fi son Sudan ta ci gaba da zama dunƙulalliyar ƙasa, to amma idan har gwamnatin sojin ƙasar ta ce za ta ci gaba da bin tsari na danniya, to kuwa “za mu zaɓi ayyana ƴancinmu.”
