Connect with us

News

Gwamnatin Najeriya ta tsaurara matakan tsaro a ofisohin INEC da ke faɗin ƙasar

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Gwamnatin Najeriya ta tura jami’an tsaro na DSS da sojoji da jami’an hukumar kashe gobara ofisoshin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta INEC domin tsaurara tsaro gabannin zaɓen 2023.

 

Advertisement

Ta kuma umarci jami’an su inganta tattara bayanan sirri domin daƙile duk wani yunƙuri na rikici ko ɓata gari a makonni masu zuwa gaba.

Mutane 20 Sun Mutu A Yayin Wata Mota Ta fada Ramin Ruwa A Pakistan

 

Advertisement

Babban Sufeta Janar na ‘yan sanda kasar, Usman Baba ne ya shaida hakan bayan tattaunawa da shugabanni jam’iyyun siyasa a hedikwatar ‘yan sanda da ke Abuja.

 

Advertisement

Rundunar ta ce a cikin mako shida, an samu rigingimu aƙalla 52 a sassa daban-daban na ƙasar da suka haɗa da Ogun da Osun.

 

Advertisement

Akwai kuma harin da aka kai wa magoya-baya a gangamin yaƙin neman zaɓe a jihohi irinsu Borno da Kaduna da Zamfara da dai sauransu.

 

Advertisement

Rundunar ta ce tana tsare da wasu da ake zargi na da hannu a waɗannan rikice-rikice, kuma za a gurfanar da su domin fuskantar hukunci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending