News
Dole Ukraine ta samu tallafi na lokaci mai tsawo – shugaban NATO
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Shugaban ƙungiyar tsaro ta NATO ya ce dole ƙasashen yamma su shirya samar da tallafi na lokaci mai tsawo ga ƙasar Ukraine, a yayin da Rasha ke nuna alamun rashin sassautawa a yaƙin da take a ƙasar.
Jens Stoltenberg ya shaida wa BBC cewa tallafin sojin zai tabbatar da ci gaba da wanzuwar ƙasar Ukraine a matsayin ƙasa mai cikakken iko tare da tilasta wa Rasha zama a teburin sulhu domin kawo ƙarshen yaƙin.
DA DUMI DUMINSA: Obasanjo Ya Bayyana Dan Takarar Shugaban Kasa Da yake So
Shugaban Rasha ya zargi ƙasashen yamma da yin amfani da Ukraine wajen lalata ƙasarsa.
Rasha ta harba makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa zuwa cikin Ukraine a jajiberin ranar sabuwar shekara.
Mista Stoltenberg ya ce sake bayyana ɗaukar sabbin sojoji da Rasha ta bayyana cikin watan Satumba, ya nuna cewa ba ta da niyyar kawo ƙarshen yaƙin.
“Dakarun Ukraine sun samu nasara a watannin baya-bayan nan, to amma mun sani Rasha na ɗaukar sabbin sojoji masu yawan gaske, da yawa daga cikin a yanzu na ƙarɓar horo”, in ji shi.
“Duka wannan alama ce da ke nuna cewa tana shirin ci gaba da yaƙin tare da yunƙurin ƙaddamar da sabbin hare-hare”.
Tun da farko, shugaban Rasha Vladimir Putin ya yi jawabin sabuwar shekara, wanda a ciki ya yaba wa dakarun ƙasar da ke yaƙi a Ukraine, yana mai cewa makomar ƙasar na hannunsu.
To sai dai takwaransa na Ukriane Volodymyr Zelensky ya zarge shi da ɓuya a bayan dakarunsa, a maimakon jagorantarsu.
