Connect with us

Sports

An dakatar da Lewandowski wasa uku jere a La Liga

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Kotun wasanni ta Sifaniya ta hukunta dan wasan gaban Barcelona Robert Lewandowski ta hanyar dakatar da shi wasanni uku a jere.

 

Advertisement

An bai wa Lewandowski jan kati a wasan da Barcelona ta yi da Osasuna gabanin tafiya hutun kofin duniya da aka fara a watan Nuwamba.

Sanyi: An samu gawar mata da miji a kulle a daki a nan Kano.

Wata kotu a Madrid ce ta dakatar da hukuncin da aka yi masa a makon jiya, wanda hakan ya bai wa dan wasan damar buga wasan da suka yi canjaras da Espanyol 1-1 a ranar Asabar.

Advertisement

 

Yanzu dai dan kasar Poland din mai shekara 34 ba zai buga wasan da Barcelona za ta yi ba da Atletico Madrid da Getafe da kuma Girona.

Advertisement

An bai wa Lewandowski katin gargadi ne har sau biyu, na biyu bayan wata mahangurba da ya yi wa David Garcia a fuska, a wasan da suka yi nasara a kan Osasuna da ci 2-1.

 

Advertisement

Hukumar kwallon kafa ta Sifaniya ce ta kara ma shi wasanni biyu kai tsaye, saboda rashin da’ar da ya rika nunawa alkalin wasa a fafatwar.

 

Advertisement

Espanyol sun fusata da hukuncin kotun da ya bai wa dan wasan damar buga wasan da suka fafata abin da ya janyo shugaban kungiyar da wasu manyansu suka ki halartar wasan nasu da Barcelona.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending