Connect with us

News

Malamai ba su iya jagoranci ba a Najeriya – Obasanjo

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce, babu wani ci gaban da aka samu a jihohin kasar da ke karkashin jagorancin mutane masu rike da matsayin farfesa ko dakta da tsoffin sojoji, har ma da malaman makarantu.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Obasanjo ya ce duk da yake an samu wasu jajirtattun shugabannin da ba su da yawa, akasarinsu ba sa iya mulki mai kyau saboda rashin samun mataimaka na gari, abin da ke hana su jagorancin da ake bukata.

Advertisement

Kotu ta yanke wa malamin islamiyya ɗaurin rai-da-rai a Legas

Tsohon shugaban ya ce, rashin tattaunawa tsakanin shugabannin da masu taimaka musu, kan haifar da gibi wajen musayar ra’ayi, matakin da ke hana samun fahimtar juna da hadin-kai wajen cimma manufar ci gaba da ake bukata.

 

Advertisement

Obasanjo ya ce, bayan kwashe shekaru 60 da samun ‘yancin kan Najeriya, har yanzu shugabannin kasar sun kasa samar da yanayin shugabanci mai inganci wanda zai samar wa kasar ci gaba da kuma magance banbance-banbancen da ake samu na kabilanci da addini da kuma shiya.

 

Advertisement

Tsohon shugaban ya ce, yadda ake tafiyar da dimokiradiyar Najeriya ya haifar da rabe-raben kawuna da mummunar alaka da rashin amince wa juna da kuma rashin kishin kasa a tsakanin jama’a da kuma al’umma a sassan kasar.

 

Advertisement

Obasanjo ya ce, abin takaici ne yadda karya da zage-zage da son kai suka mamaye yakin neman zaben da ake gudanarwa yanzu haka, maimakon gabatar da shirin da ake da shi na gina kasa.

 

Advertisement

A halin yanzu dai jihohin Borno da Cross Rivers ne kawai ke da masu rike da mukamin farfesa da ke jagorancin su a matsayin gwamnoni, yayin da ake da wasu masu mukamin dakta.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending