Connect with us

News

Allah ya yi wa Professor Ibrahim Halilu Umar, rasuwa

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

 

Advertisement

Babban masanin kimiyyar nan, kuma babban Farfesa a jami’ar Bayero, Farfesa H.I Umar ya rasu a yammacin wannan rana.

 

Advertisement

Farfesa I.H Umar ɗaya ne daga cikin fitattun masana kimiyyar Fizika (Physics) da lissafi a faɗin Najeriya.

Likitoci sun dakatar da yajin aikin da suka shirya yi a Najeriya

Marigayin ya taɓa zama shugaban jami’ar Bayero daga shekarar 1979 zuwa 1986. Ya yi digirinsa na farko a fannin kimiyyar Fizika daga jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, sannan ya tsallaka ƙasar Amurka inda ya yi digirinsa na biyu a jami’ar Arewacin Illinois a 1974, sannan ya kammala digirinsa na uku daga jami’ar East Anglia a ƙasar Ingila.

Advertisement

 

Ya kasance ɗaya daga cikin muhimman farfesoshi biyar na farko da suka fara samun matsayin “Emeritus” daga jami’ar Bayero a Kano.

Advertisement

 

Marigayin ya wakilci Najeriya da manyan hukumomi na duniya a lokuta daban-daban a tarurruka da kwamiti i da suka shafi kimiyya a faɗin duniya.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending