Connect with us

News

Zaɓen 2023: Za a rufe iyakokin Najeriya na sa’a 24

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin rufe iyakokin ƙasar na sa’a 24 gabanin babban zaɓen ƙasar da ke tafe a ranar Asabar.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Hukumar Shige da Fice ta Najeriya ta fitar a shafinta na twita wanda ya samu sa hannun shugabanta, Isah Jere Idris.

Advertisement

Manchester United Ta Tankado Keyar Barcelona Daga Europa

Sanarwar ta ce daga gobe Asabar za a rufe dukkan iyakokin ƙasar na ƙasa har zuwa ranar Lahadi 26 ga watan Febrairun 2023.

Idris Jere ya buƙaci dukkan shugabannin hukumar da ke kan iyakoki da su tabbata an bi sahun wannan umarni.

Advertisement

Ya ce hukumar a shirye take wajen ganin ta bayar da gudummawa na ganin an gudanar da zaɓukan ƙasar lami lafiya.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending