News
Wata Tirela Maƙare Da Kaya Ta Ƙwace Ta Afka Masallaci A Suleja
Wata trela makare da madara na gari ta kutsa kai cikin wani masallaci a Suleja, Jihar Neja, a ranar Talata, inda a kalla mutane uku suka makale, kamar yanda jaridar Daily Trust ta rahoto.
Hatsarin ya faru ne misalin karfe 6 na safiyar lokacin da mutane da dama sun fice daga masallacin bayan sallar Asuba.
Yan bijilante za su kama saurayi da budurwa da ke zance a lokacin sallar Tahajjud
A cewar shaidun gani da ido, trelan ta fada a sashin baya na masallacin inda mata da yara ke sallah.
mutane uku, ciki har da yaro, sun makale a baraguzan kuma sun jikkata.
Advertisements
