Connect with us

News

Tinubu ya bar Najeriya zuwa Turai, kwana 19 Kafin a rantsar dashi

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Advertisement

 

 

Advertisement

 

A ranar Larabar da ta gabata ne zababben shugaban kasa, Bola Tinubu ya bar Najeriya zuwa kasashen Turai domin ziyarar aiki.

Advertisement

 

 

Advertisement

Tinubu zai daidaita shirye-shiryen mika mulki, shirye-shirye, da zabin manufofinsa tare da wasu manyan mataimakansa ba tare da raba hankali ba.

 

Advertisement

Ya kamata mawaka su maida hankali akan wakokin fadakarwa bana sharholiya ba….JAMILA MUHAMMAD IBRAHIM.

A yayin ziyarar, zababben shugaban kasar zai tattauna da masu zuba jari da sauran manyan abokan hulda da nufin tallata guraben zuba jari a kasar da kuma shirye-shiryen gwamnatinsa na samar da yanayi mai kyau na kasuwanci ta hanyar manufofi da ka’idoji.

 

Advertisement

 

A wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Tunde Rahman ya fitar ta ce: “Tuni, an jera tarurruka da masu ruwa da tsaki a harkokin kasuwanci na Turai da suka hada da masana’antu, noma, fasaha da makamashi.

Advertisement

Asiwaju Tinubu na fatan gamsar da su kan shirin Najeriya na yin kasuwanci a karkashin jagorancinsa ta hanyar hadin gwiwar da za ta amfana da juna kan samar da ayyukan yi da kuma samun kwarewa.

 

Advertisement

“Fara farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar ya zama babban ginshiƙi na ajandar sabunta bege na Tinubu kuma taron yana cikin ƙoƙarinsa na sake dawo da martabar Nijeriya a cikin tsarin tattalin arzikin duniya da kuma samar da damammaki masu ƙarfafawa ga dumbin matasan ƙasar.

 

Advertisement

“Shugaban kasa mai jiran gado ya yi alkawarin kawo karshen wannan al’amari kuma ziyarar tana nuni ne da jajircewarsa kan wannan alkawari domin tuni ya fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki a duniya a muhimman fannonin tattalin arziki da tsaro.”

 

Advertisement

Tun kafin ya bar kasar, Tinubu ya gana da ‘yan takarar majalisar wakilai da ‘yan takarar shugaban kasa da mataimakinsa wadanda jam’iyyarsa ta All Progressives Congress, Hon. Tajudeen Abbas and Hon. Benjamin Kalu, wanda kwamitin hadin gwiwa na majalisar ya gabatar masa.

 

Advertisement

Ana sa ran zai dawo nan ba da jimawa ba don shirye-shiryen rantsar da shi a hukumance a matsayin shugaban Najeriya na 16 a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending