Business
Airtel Ya Kaddamar da 5G A Jihohi 3,ciki harda Abuja
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
A ranar Litinin ne kamfanin sadarwa na Airtel Nigeria ya kaddamar da tsarin sadarwar wayar salula na 5G a jihohi uku ciki harda abuja
Kaddamarwar da kamfanin na Airtel ya kawo adadin masu amfani da layin sadarwa da ke ba da sabis na 5G zuwa uku a kasar.
Tun farko dai MTN Nigeria da Mafab sun kaddamar da sabuwar fasahar sadarwa a bara da farkon wannan shekarar.
Yayin da MTN ke buda baki a jihohi da dama, har yanzu Mafab (MCom) bai kaddamar da ayyukansa na 5G ba tun da aka kaddamar da shi a watan Janairu.
Amma da yake magana yayin kaddamar da kafafen yada labarai da aka gudanar a Legas, Babban Jami’in Kamfanin Airtel na Najeriya, Carl Cruz, ya ce hanyar sadarwar za ta kawo dimokuradiyya ta ayyukan 5G a Najeriya.
Cruz ya ce masu amfani da layin Airtel za su ji daɗin sabis na bayanai cikin sauri da kuma sake fasalin ayyuka a wasu sassan tattalin arzikin da suka haɗa da telemedicine, noma, da sauransu.
Jaridar Daily trust ta rawaito cewa Sabbin bayanai daga Hukumar Sadarwa ta kasa (NCC) sun nuna cewa a halin yanzu Airtel na da kashi 27.01 cikin 100 na masu amfani da wayar salula na kasa.
-
News5 days ago
Magoya Bayan APC Sun Yi Allah-Wadai da Rushe Gidan Sani Sha’aban, Sun Buƙaci a Yi Adalci
-
News4 days ago
Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Wayoyi Ta Buƙaci NCC Ta Dakatar Da Tsarin Tantance Wayoyi Na DMS Tsawon Kwanaki 90
-
News7 days ago
AWOHI Ta Raba Kayan Tallafi A Gidan Kula Da Tsofaffi Na Shahuci Dake Kano

