News
SUDAN:An kai hare-hare kan ofisoshin jakadancin kasashen waje a Sudan
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Ana ci gaba da kai hare-hare da sace-sacen kaya a ofisoshin jakadanci na kasashen waje a Sudan, inda Aljeriya ta kasance kasa ta baya bayan nan da ta yi korofi.
A ranar Laraba, ma’aikatar harkokin wajen Aljeriya ta ce an kai hari gidan jakadanta da ke babban birnin kasar, Khartoum.
Ambaliyar ruwa ta shafi ‘yan Najeriya sama da miliyan 4 a 2022 – NEMA
Ta ce harin ya saba wa dokokin kasa da kasa, ta kuma yi kira ga mahukuntan Sudan da su hukunta wadanda suka aikata laifin.
Zimbabwe ita ma ta yi Allah wadai da harin da aka kai ofishin jakadancinta da kuma gidan jakadanta a birnin Khartoum, inda kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ya zargi dakarun RSFF da hannu a cikin harin.
Livit Mugejo ya ce “Muna da rahotannin cewa galibin kadarorin kasashen ne aka kai wa hari. Wannan babban laifi ne, a yi amfani da yaki wajen wawushe kadarorin jami’an diflomasiyyarmu da ofishin jakadancinmu da ke can.”
A ranar Talata, Mauritaniya ta ce wasu mahara dauke da makamai sun kai hari ofishin jakadancinta da ke birnin Khartoum tare da wawashe kaya.
Kafofin yada labaran Mauritaniya sun ce an sace akalla motoci uku da jakadan da ma’aikatansa ke amfani da su.
Sojojin Sudan sun sha dora alhakin hare-haren kan ofisoshin diflomasiyya a kan kungiyar RSF, wacce ta musanta hannu cikin aikata laifin.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News6 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News3 days ago
Gwamna Abba Ya Ayyana Murtala Sule Garo A Matsayin Wanda Zai Yi Masa Takarar Mataimakin Gwamna A Zaɓen 2027
