Connect with us

News

Yan Bindiga Sun Harbe Fasto A Cocin Ogun

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Wasu ’yan bindiga sun kai farmaki majami’ar RCCG da ke Abule-Ori a Karamar Hukumar Obafemi Owode ta Jihar Ogun, inda suka kashe Fasto suka kuma yi awon gaba da mabiyansa.

Daily trust ta rawaito cewa an kai harin ne da daren Asabar, lokacin da mutanen ke tsaka da addu’o’in dare a cikin cocin.

Kwamandan rundunar So-Safe Corps da ke Jihar, Soji Ganzallo ne ya tabbatar da kai harin da safiyar Lahadi.

Sai dai ya ce jami’ansu sun sami nasarar kubutar da mambobi bakwai na cocin sannan suka kashe daya daga cikin maharan yayin ba-ta-kashin da suka yi.

Advertisement

SERAP ta buƙaci Tinubu da ya bayyana yadda aka kashe biliyan 400 ta tallafin man fetur da ya ce an cire

A cikin wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai na rundunar a Jihar, Moruf Yusuf ya fitar, Soji ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 12 na daren Asabar, 1 ga watan Yuli.

A cewarsa, an dora wa dakarun rundunar alhakin ceto mutanen da ransu, kuma ba tare da an ji musu ko da kwarzane ba.

Ya ce hakan ce ta sa suka shiga aiki nan take wanda har ya kai su ga samu nasarar kubutar da mutanen.

 

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending