Connect with us

News

Yan daba sun kashe wani jami’in dan sanda a kano.

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN 

 

Yan daba sun kashe wani jami’in dan sanda yayin da wani fada tsakanin kungiyoyin ’yan daba guda biyu a unguwar Yakasai da ke birnin Kano.
Lamarin, a cewar wani ganau, ya faru ne wajen misalin karfe 6:00 na yammacin Talata, lokacin da wani dan daba da ya sauka daga babur din Adaidaita Sahu a kusa da Asibitin kwararru na Maurtala Muhammad da ke Kano, abokan fada kuma suka hau shi da sara.

Allah Gwani | Yin Sallah Na Rage Ciwon Baya — Bincike.

Majiyar, wacce ba ta amince a bayyana sunanta ba, ta ce, bayan saukar mutumin ne daga kan babur din sai wasu ’yan dabar da ba sa ga maciji suka far masa da makamai.

“Sai da ’yan sanda suka kwashe kusan minti 10 kafin su tarwatsa su, inda ’yan dabar suka juyo kan ’yan sanda suka fara jifan su.

“Lokacin da ’yan sandan ke kokarin guduwa ne sai daya daga cikinsu ya fado daga kan mota, inda nan take ’yan dabar suka hau saran shi, ba ji ba gani. Tuni ma ya riga mu gidan gaskiya,” in ji majiyar.

Advertisement

Majiyar ta kara da cewa an shafe tsawon kwanaki ana fuskantar fadan daba a unguwar.

Da wakilinmu daily trust ya tambayi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce har yanzu ba su samu rahoton kisan ba, amma suna nan suna bincike a kai don gano gaskiyar abin da ya faru.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending