Connect with us

News

Yan bindiga sun sace Masu Aikin Titin Kaduna-Kano Su 4 A Tashar Yari

Published

on

Yan bindiga

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Ana fargabar ’yan bindiga sun sace wasu ma’aikatan kamfanin gine-gine su hudu a garin Tashar Yari da ke Karamar Hukumar Makarfi ta Jihar Kaduna.

Wasu mutum biyu kuma sun ji raunuka kuma yanzu haka suna samun kulawa a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika, Zariya.

Advertisement

An Bukaci Amurka Ta Hana Abba Izinin Shiga Kasarta Saboda Rushe-Rushe A Kano

An kai harin ne ranar Asabar.
A cewar wata majiya a yankin, maharan sun kewaye ginin da ma’aikatan ke zaune ne, sannan suka yi awon gaba da mutanen.

Rahotanni na nuni da cewa lamarin ya faru ne a kan babban titin Kaduna zuwa Zariya zuwa Kano, inda ma’aikatan ke cikin masu aikin gina titin.

Advertisement

Majiyoyi da dama a garin Makarfi sun tabbatar da faruwar harin, ciki har da wani shugaban al’umma da ya nemi a sakaya sunansa.

A cewar shugaban, maharan sun isa yankin ne cikin dare lokacin ana ruwan sama, inda suka kai wa mutanen hari ba tare da wata matsala ba.

Advertisement

Ya kuma ce, “An sace mutum hudu, wasu biyu kuma sun samu raunuka, kuka nan take aka garzaya da su asibiti domin samun kulawa.”

Sai dai duk kokarin wakilinmu na jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Mohammed Jalige, ya ci tura saboda bai amsa kira wayarsa ba.

Advertisement

Kazalika, har zuwa lokacin hada wannan rahoton bai amsa sakon kar-ta-kwanan da aka tura masa ba.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending