Connect with us

News

Kasar China Ta Hana Yara Amfani Da Yanar Gizo Da Daddare.

Published

on

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.

Hukumar kula da amfani da shafukan yanar gizo ta kasar China ta kafa wata sabuwar doka da za ta takaita tsawon lokacin da yara ke shafewa suna amfani da wayoyinsu a yanar gizo.

Advertisement

Matakin dai zai kawo babban cikas ga kamfanoni irin su Tencent da ByteDance, wadanda su ne manyan masu shafukan intanet da wasannin da ake yi a yanar gizo a kasar.

Kungiyar SERAP ta kai karar Tinubu kan rashin fitar da bayanan kashe biliyan 400

A ranar Laraba ce dai hukumar ta wallafa kundin sabuwar dokar a shafinta na yanar gizo, inda ta ce a yanzu, ba za a kyale kananan yara su yi amfani da intanet da daddare ba.

Advertisement

Kazalika, ta ce yara masu shekara 16 zuwa 18 a yanzu za su rika amfani da yanar gizo ne kawai na tsawon awa biyu kacal.

Bugu da kari, yara masu shekara 8 zuwa 15 za su rika amfani da yanar gizo t na awa daya kacal, ’yan kasa da shekara 8 kuwa za su iya shafe minti 40 ne kawai a kullum.

Advertisement

Dokar ta ce wasu shafuka da kawai aka yi ittifakin suna da amfani ga yara za a kyale su su yi amfani da su sama da wannan lokacin. Sai dai hukumar ba ta yi bayani a kan shafukan ba.

Wannan sabon matakin dai shi ne irinsa na baya bayan nan da gwamnatin China take sanyawa domin rage yawan sabon da yara ke yi da intanet, matsalar da ta ce ta tasam ma zama ruwan dare.

Advertisement

Ko a shekara ta 2019, sai da gwamnatin ta rage tsawon lokacin da yara za su iya shafewa suna wasanni ta intanet zuwa minti 90.

A shekara ta 2021 kuwa, an dada tsaurara matakan inda aka mayar da awa dayan kawai a ranakun Juma’a da Asabar da Lahadi da kuma ranakun hutu.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending