News
Shugaba Tinubu Ya Kaddamar Da Kwamitin Gyaran Haraji
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu ya kaddamar da kwamitin shugaban kasa kan manufofin kasafin kudi da yi wa fannin haraji garambawul
Channels ta rawaito cewa an gudanar da bikin kaddamarwar ne a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Talatar nan.
Kasar nan Ce Kan Gaba A Bangaren Masu Zaman Kashe Wando A Duniya
Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan ayyuka na musamman, sadarwa da dabaru, Dele Alake, a cikin wata sanarwa a ranar 7 ga watan Yuli ya sanar da kafa kwamitin da shugaban ya kaddamar.
Alake ya lura cewa kwamitin zai kasance karkashin jagorancin Fiscal Policy Partner kuma shugaban haraji na Africa a PriceWaterhouseCoopers (PwC), Taiwo Oyedele.
Kwamitin ya ƙunshi ƙwararru daga sassa masu zaman kansu da na gwamnati kuma za su ɗauki nauyin sassa daban-daban na sake fasalin dokokin haraji, tsara manufofin kasafin kuɗi da daidaitawa, daidaita haraji, da sarrafa kudaden shiga.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
