News
Kamfanin Mai na NNPCL ya ce maganar ƙara kuɗin Man fetur ba gaskiya bane.
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN.
Kamfanin Man Fetur na Ƙasa NNPCL ya ce batun da ake ta yamaɗiɗi a kai na cewa za a ƙara farashin man fetur a ƙasa ba gaskiya bane.
Cikin wani saƙo da kamfanin ya wallafa a shafin X da a baya aka sanshi da twitter, ya ce kamfain mai da ma dillalansa daga ƙasashen ƙetare ba su da wata aniya ta ƙara masa kuɗi.
Yanzu-Yanzu:Hukumar DSS Ta Gurfanar Da Emefiele Kan Sabbin Laifuka 20
“Ya ku abokan hulɗarmu, ba mu da wata aniya ta ƙarawa man fetur kuɗi kuma muna jin dadin harkar da kuke yi da mu’”
“Don haka ku ci gaba da sayan man fetur a farashi da ya zo daidai da buƙatunku a gidajen man dake duk inda kuke a fadin kasarnan”
Idan za a iya tunawa dai a ranar Lahadi ne yan kasuwar man suka bayyana cewa farashinsa ka iya tashin gwauron zabi zuwa naira 680 zuwa naira 720 muddin farashin dala ta ci gaba da hauhawa daga naira 910 zuwa naira 950 a kasuwannin chanji.
Kazalika sun ayyana cewa an tilasta wa dillalan man dake shigo dashi daga ƙetare zama cikin shiri na ƙara farashin sakamakon ƙarancin kudaden kasar waje da ake Ambani da su wajen ahigo da man.
Wannan gargaɗi na zuwa jim kaɗan bayan da farashin dala ke ci gaba da tashin gwauron zabi inda aka saidata a kan Naira 945 a ranar Juma’a da ta gabata.
Wakilin Kamfanin Jaridar Daily Post ya tuntuɓi mai magana da yawun kamfanin NNPC Garba-Deen Muhammad kan yiwuwar ƙara farashin man fetur ɗin toh amma ya shaida masa cewa zai zurfafa bincike kana daga bisani ya maida jawabi.
Toh sai dai har lokacin haɗa rahoton Garba-Deen bai ce uffan ba bacin abinda kamfanin ya wallafa a shafinsa na X.
