Connect with us

News

Rushewar Gadar Takai ta haifar da matsananciyar wahala da kuma tabarbarewar tattalin arziki ga mazauna kauyuka hudu A Kano

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI.

 

Advertisement

Gadar da ta ruguje a garin Fajewa da ke karamar hukumar Takai a jihar Kano na haifar da matsananciyar wahala da kuma tabarbarewar tattalin arziki ga mazauna kauyuka hudu da abin ya shafa, kamar yadda binciken Jaridar Indaranka ya nuna.

Gadar da ta ruguje ta ratsa kogin Takai na da tazarar kilomita 10 kacal daga hedkwatar karamar hukumar Takai, kuma ta hada kauyuka hudu da kasuwanni biyu a yankin.

Advertisement

Sarkin Kano Ya Amince da Nadin Sabbin Wakilai A kasuwanni Jahar Kano.

Jaridar Indaranka ta rawaito cewa Kauyukan da abin ya shafa sun hada da Fajewa, Birnin Bako, Tumbushi, da Gidan Malam duk a cikin karamar hukumar Takai

Ziyarar da wakilinmu ya kai garin ya nuna yadda matasa suke dauku mata da yara kanana a kafadarsu domin ketare kogin da ya malala don gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Advertisement

Wani mazaunin kauyen, Malam Audu Nabawa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na News Point Nigeria cewa rugujewar gadar ta hana mazauna kauyukan garuruwan hudu damar zuwa asibitoci da kasuwanni da makarantu.

“Gadar ta ruguje ne kimanin makonni hudu da suka gabata kuma gwamnati ta sani amma ba a yi komai ba.

Advertisement

Ita ma da take magana, wata mai sana’ar dinki a kauyen Birnin Bako, Mariya Tasi’u, ta ce matasan sun koma daukar su a kafada domin a matsayinsu na matan garuruwan hudu ba su da wani zabi.

“Ba mu da wani zabi, muna bukatar mu je kasuwa da asibitoci da garuruwan da ke makwabtaka da mu don samun wasu abubuwan yau da kullun, hanyar da za mu bi ta hanyar tsallaka kogi a kafadar daya daga cikin yaran.

Advertisement

“Suna karban Naira 200 ko N300 a kowane yaro ko kuma mata yayin da farashin Mashin ko kuma kaya akan N500 zuwa N700 .

A nasa bangaren, babban limamin masallacin Fajewa, Malam Umar Babba ya nuna rashin jin dadinsa ga mahukunta a matakin jiha da na kananan hukumomi bisa abin da ya kira sakaci da gangan na sanya al’ummarsa cikin wahala sakamakon rugujewar gadar.

Advertisement

Da aka tuntubi dan majalisar da ke danne mazabar Takai a majalisar dokokin jihar Musa Ali Kachako ya ce ya gabatar da kudirin gyara gadar kuma yana jiran amsa daga gwamnati.

Daga nan sai ya roki hukumomin gaggawa da abin ya shafa a jihar da su gaggauta duba lamarin gadar da ta ruguje domin dakile radadin al’ummar da lamarin ya shafa.

Advertisement

Sai dai har yanzu Sakataren zartarwa na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Kano (SEMA), Alhaji Isyaku Abdullahi Kubarachi, bai amsa tambayoyin da aka tuntube shi kan lamarin ba har zuwa lokacin

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending