Connect with us

News

Za’a Fuskanci Mamakon Ruwan Sama A Jahar Kano Da Wasu Jahohi 20

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI

 

Advertisement

Hukumar kula da yanayi ta kasa, Ta yi hasashen samun mamakon ruwan sama kamar dab akin kwarya a wasu bangarori na Kasar nan kamar Kano da Kwara da Niger a yau Juma’a da kuma ranar Asabar, Yayin da kuma za’a samu matsakaicin ruwan sama a wasu jahohin kasar nan guda 20.

Bayanin hakan na kunshe ne cikin rahoton hasashen yanayi da hukumar ta fitar a ranar Alhamis.

Advertisement

Taiwo Awoniyi Na Cikin Masu Takarar Gwarzan Dan Wasan Premier Na Watan August

Rahoton ya baiyana cewar, za’a iya fuskantar mamakon ruwan sama a cikin sa’oi 24, sannan kuma wasu wuraren za’a samu matsakaicin ruwan sama, yayin da za’a iya fuskantar tumbatsar koguna da zaizayar kasa, da kadawar iska mai karfi da Cida da kuma tsawa.

Hukumar kula da yanayin ta kasa ta baiyana cewar jahohin da za’a iya fuskantar matsakaicin ruwan sama a gobe Asabar, sun hada da wasu bangarori na jihar Ribas sai Delta da Bayelsa da AKwa Ibom da Cross River da Yobe.

Advertisement

Sauran sune Benue da Jigawa da Katsina sai Zamfara da kuma jahar Sokoto

A wani labarin kuma Taiwo Awoniyi Na Cikin Masu Takarar Gwarzan Dan Wasan Premier Na Watan August

Advertisement

Gwamnan jahar Ondo, Rotimi Akeredolu ya dawo gida Najeriya bayan dogon hutun da ya dauka domin duba lafiyarsa a kasar Jamus.

Gwamnan ya bar Najeriya watanni ukku da suka gabata domin duba lafiyarsa a kasar ta Jamus.

Advertisement

Shugaban masu rinjaye a zauren majalisar dokokin jihar Ondo, Wole Ogunmolasuyi, wanda ya tabbatar da dawowar gwamnan ga wakilinmu, Ya ce a yanzu haka gwamnan yana gidansa dake birnin Badun.

Kazalika maid akin gwamnan, Uwargida Betty ta tabbatar da dawowar mai gidan nata a shafinta na X, inda ta wallafa hotonsa a cikin jirgin sama.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending