News
An Kama Wasu Kasurguman Masu Garkuwa Da Mutane 2 Da Kuma Yan Ta’adda 89 A Kaduna
DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN
Dakarun sojoji na musamman a Jihar Filato sunce jami’an su sun kama wasu kasurguman masu garkuwa da mutane 2 da kuma yan ta’adda 89 a jihar da kuma Kaduna mai kwabtaka da ita.
Jami’an yada labarai na rundunar a jihar Filato Kaftin Oya James shine ya bayyana haka jiya a Jos babban birnin jihar.
Majalisar Dattawa ta fara bincike kan kisan ‘yan Nijeriya 250 a kasar Habasha
James yace dakarun sun gudanar da ayyuka a wurare mabanbanta cikin makonni 2 kuma sun samu nasara.
Ya kuma kara da cewa dakarun sun samu nasarar kama wasu mutane 4 da ake zargin masu garkuwa da mutane ne, tare da kubutar mutane masu yawa da aka garkuwa da su, da kwato shanun sata.
Wadanda ake zargin suna da hannu a sace dalibai 7 na jami’ar jihar Filato da a ka yi watan Yulin wanna shekarar.
Jami’an sun samu nasarar kwato bindiga kirar AK-47 da alburusai a hannun bata garin. Kwamandan dakarun ya tabbatar da cewa za’a gurfanar da wadanda ake zargin a gab kotu da zarar sun kammala bincike.
A wani labarin kuma Majalisar Dattawa ta fara bincike kan kisan ‘yan Nijeriya 250 a kasar Habasha
Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.
Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.
A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.
Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.
