Connect with us

Business

Majalissar Dattawa Ta Bukaci A Mika Matatun Man Fetur Ga Hannun Masu Zuba Jari

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Majalisar dattawa ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta mayar da matatun man kasarnan hannun masu zuba jari domin Jinginarwa.

Shugaban kwamitin majalisar dattawa mai kula da harkokin kudi, Sanata Sani Musa na jam’iyyar APC daga Neja ta Gabas ya yi wannan kira ne a karshen mako a Abuja.

Gwamnatin Tarraya Ta Biya Billiyan 169.4 Amatsayin Tallafin Man Fetur A Watan Agusta 2023

Musa ya amsa tambayoyi daga ‘yan jarida akan hanyar cigaban Najeriya, shekaru 63 da samun ‘yancin kai.

A cewarsa, matatun man sun zama nauyi ga gwamnati idan aka yi la’akari da yadda aka gaza gyara su.

Advertisement

A wani labarin kuma Gwamnatin Tarraya Ta Biya Billiyan 169.4 Amatsayin Tallafin Man Fetur A Watan Agusta 2023

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending