Connect with us

Business

Bankin Duniya ya ce kudin Nijeriya yana cikin kudaden Afirkan da darajasu ta ragu

Published

on

kudin Nijeriya wato Naira

DAGA KABIRU BASIRU FULATAN

 

Advertisement

Bankin Duniya ya ayyana kudin Nijeriya wato Naira, cikin kudaden da suka fi rasa darajarsu a fadin nahiyar Afirka. Naira ta rasa kashi 40 cikin 100 na ƙarfinta idan aka kwatanta da dalar Amurka bayan da aka karya darajarta a watan Yuni.

A cewar wani rahoto mai taken ‘Africa’s Pulse’, wanda ya yi sharhi kan batutuwan da za su shafi tattalin arzikin Afrika a nan gaba, na watan Oktoban nan, an bayyana cewa Naira ta rasa kashi 40 cikin 100 na ƙarfinta a musayar dalar Amurka.

Advertisement

An Hana Sayar Da Littafin Queen Primer A Fadin Jihar Kano 

Rahoton na Bankin Duniya ya ce a bana Naira da kuma kudin kasar Angola, wato Kwanza su ne suka fi rasa daraja a yankin Afirka, daga farkon shekara zuwa yau. Hakan ya faru ne sakamakon wasu matakai da manyan bankunan kasashen suka dauka.

 

Advertisement

Matakin da Babban Bankin Nijeriya ya dauka na barin Naira ta yi gogayya da dalar Amurka da sauran manyan kudade a kasuwar hada-hadar kudade, ya haifar da gagarumar faduwar darajar Naira daga N473.83 kan duk $1, zuwa sama da N800 duk $1.

 

Advertisement

Rahoton ya nuna cewa faduwar ta yi ta faruwa ne a hankali, tun watan Maris na shekarar 2020, amma kuma sai abin ya yi tsamari bayan da Babban Bankin Nijeriya ya janye tallafin da yake bai wa Naira. Daga nan ne tazarar farashi tsakaninsu ta karu matuka.

 

Advertisement

A Afrika dai, sauran kudaden da suka fuskanci faduwar daraja a 2023 sun hada da kuɗaɗen:

 

Advertisement

Sudan ta Kudu (faduwar kashi 33%)

Burundi (faduwar kashi 27 %),

Advertisement

Jumhoriyar Dimukradiyyar Congo (faduwar kashi 18%)

Kenya (faduwar kashi 16%)

Advertisement

Zambiya (faduwar kashi 12%)

Ghana (faduwar kashi 12%)

Advertisement

Rwanda (faduwar kashi 11%).

A Wani labarin kuma An Hana Sayar Da Littafin Queen Primer A Fadin Jihar Kano 

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

 

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

 

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

 

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending