Business
Kamfanonin Jiragen Sama Sun Bukaci Gwamnatin Najeriya Ta Sahale Musu Lasisin Shigo Da Man Jiragen Sama
DAGA KABIRU BASIRU FULATAN
Kamfanonin jiragen sama na cikin gida a karkashin inuwar kungiyar masu kamfanin jiragen sama ta Najeriya na neman gwamnatin tarayya ta ba su damar samun lasisin shigo da man jiragen sama, mai suna JetA1.
Sun kuma bukaci gwamnati ta ba su damar samun chanjin kudaden waje daga babban bankin kasa domin baiwa masu sufurin damar sauke nauyin da ya rataya a wuyansu na matafiya.
Jami’an Tsaro Sun Hallaka ‘Yan Fashin Daji 60, Sun Ceto Mutum 29 A Bauchi
Shugaban kungiyar ta AON, Alhaji Abdulmunaf Yunusa ne ya yi wannan kiran a madadin mambobinsa yayin ziyarar ban girma da suka kai wa ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, domin bayyana masa kalubalen da suke fuskanta.
Da yake mayar da martani, Keyamo ya yiwa masu kamfanonin jiragen sama alkawarin cewa ma’aikatar za ta hada kai da CBN domin ganin yadda za su rika samun chanjin kudaden waje cikin sauki.
Sai dai ya bukaci masu kamfanonin da su guji jinkirta tashin jirgin domin nan ba da dadewa ba zai fara aiwatar da dokar biyan diyya ga matafiya idan jirginsu ya yi jinkiri ba tare da wani dalili ba.
-
Opinion5 days ago
Wakilcin Mataimakin Gwamna Garo A Taron Tsaro Na Arewacin Najeriya Abin A Yabawa Gwamna Yusuf Ne
-
News1 day ago
Karuwar Ta’ammuli Da Miyagun Ƙwayoyi Tsakanin Mata Na Barazana Ga Makomar Iyali – Masana
-
News7 days ago
Wasu Da Ake Zargi ‘Yan ISWAP Ne Da Iyalansu Sun Mika Wuya Ga Dakarun Soji
