Connect with us

Politics

Gwamnonin PDP za su tattauna don sulhunta Gwamna Fubara da Wike

Published

on

DAGA YASIR SANI ABDULLAHI 

Saɓanin wani sauyi ko canjin al’amari, ana sa ran a yau Talata gwamnonin PDP za su tattauna don ganin sun sulhunta takun saƙar da ke tsakanin Ministan Abuja Mr. Wike da kuma gwamnan jihar Ribas Similanayi Fubara.

Advertisement

Gwamnonin sun bayyana rashin jin daɗinsu akan yanda siyasar jihar ke gudana. Shi yasa suke ganin ya dace su tattauna don warware matsalar cikin fahimtar juna.

Kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin jihar Gombe sun rufe majalisar dokokin jihar

Jihar Ribas dai ta PDP ce, kuma Wike shima ɗan PDP, sai dai a yanzu haka Minista ne a gwamnatin APC ta Tinubu.

Advertisement

Sai dai rikicin da ya kuma ɗaukar salo na tsige shugaban masu rinjaye na majalissar da kuma ƙone wani sashi na majalisar, gami da samar da kakakin majalissar har mutane biyu, su suka ƙara tabbatarwa gwamnonin dole su dubi lamarin kafin lokaci ya ƙurace.

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa Idan dai za a iya tunawa Wike shi ya jagoranci komai da komai don ganin gwamna Fubara ya zama gwamna a jihar mai arziƙin man fetur, in da ya yi nasarar zama gwamna ranar 18 ga watan Maris ɗin shekarar 2023.

Advertisement

A wani labarin kuma Kungiyar ma’aikatan majalisar dokokin jihar Gombe sun rufe majalisar dokokin jihar

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Advertisement

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Advertisement

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending