News
Da Gangan Aka Hana Lauyoyinmu Kwafin Hukuncin Shari’ar Zaben Gwamnan Kano – NNPP
DAGA YASIR SANI ABDULLAHI
Mai rikom mukamin shugaban jam’iyyar NNPP na kasa, Abba Kawu Ali, ya bayyana damuwa akan gazawar kotun daukaka kara na sakin takardun hukuncin shari’ar zaben gwamnan Kano ga tawagar lauyoyin Jam’iyyar.
Ali, a cikin wata sanarwa, ya ce batutuwan kwanaki da lokaci suna da matukar muhimmanci wajen shirye-shiryen daukar matakin daukaka kara a irin wannan yanayi.
Ya nunar da cewa mai kara yana da damar kwanaki 14 kawai don kammala shirinsa, kuma asarar kwanaki 4 daga cikin wadannan kwanaki 14 kamar kafa tarko ne ga mai kara.
Ya kuma yi zargin cewa da gangan ake kokarin kawo cikas ga jam’iyyar NNPP.
Ya nanata kudurin jam’iyyar na yin aiki a cikin tsarin doka don dawo da hakkokinta a kotun koli.
A wani labarin kuma Gobe Talata Kotun Daukaka Kara Zata Raba Gardama A Adamawa
Shugaban ƙungiyar Hamas, Ismail Haniyeh, ya ce su na dab da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da Isra’ila.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafin Telegram, Haniyeh ya ce Hamas ta aika wa Qatar sako wadda ke ƙoƙarin shiga tsakani a tattaunawar kan sako ƙarin waɗanda Hamas ta yi garkuwa da su daga kudancin Isra’ila.
Majiyar masu shiga tsakanin sun ce wannan karon akwai kwarin gwiwa kan batun, za a kuma sako wasu daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su, inda ita kuma Isra’ila za ta dakatar da wuta na kwanaki uku zuwa biyar.
Tuni shugabar ƙungiyar agaji ta Red Cross ta tafi Qatar domin tattauna batun sakin Isra’ilawan.
