Connect with us

News

Akalla jarirai 10 suka mutu dalilin fama da tsananin yunwa a sansanin ‘yan gudun hijira dake Abuja – Kungiya

Published

on

Sansanin ‘yan gudun hijira

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN 

 

Advertisement

Akalla jarirai 10 ne suka rasu a dalilin fama da tsananin yunwa a sansanin ‘yan gudun hijira dake Waru a Babban Birnin Tarayya Abuja.

Shugaban kungiyar mata dake sansanin sansanin Fatima Mohammed ta sanar da haka da take ganawa da Kamfanin Dillancin Labarai  na kasa NAN ranar Litinin a Abuja.

Advertisement

Majalisar Zartarwar Nijeriya ta amince da karbo lamunin gata na dala biliyan daya daga Bankin Raya Kasashen Afirka 

Fatima ta ce tun da aka kafa wannan sansani a 2013 ake rasa Jarirai saboda tsaninin yunwa da sukan yi fama da ita.

Ta ce yunwa na daga cikin matsalolin dake ci wa iyaye tuwo a kwarya a sansanin.

Advertisement

“A yanzu haka wata mai jego ta rasu a dalilin yunwa.

“Rashin asibiti, rashin tsaftataccen ruwa da rashin bandaki na daga cikin matsalolin da muke fama da shi a sansanin.

Advertisement

“A dalilin rashin bandakuna mata da dama na kamuwa da cututtuka da a dalilin haka bas iya haihuwa ma kwatakwata.

Premium Times ta ruwaito cewa Fatima ta yi kira ga ma’aikatar jinkai da yaki da fatara da ta yi gaggawar kawo musu dauki a wannan sansani.

Advertisement

“Zuwa yanzu mutum kusan 3,870 ke zama a wannan sansani.

“A da mukan samu tallafi daga kungiyoyi, da kuma Shugaban hukumar ‘Yan Gudun Hijira Imaan Suleiman kan tallafa mana amma tun da suka tafi muka daina samun wadannan tallafi.

Advertisement

“Sannan ministan ma’aikatar Jin Kai Sadiya ta kan kawo nata tallafin domin mata ta hanyar koya musu sana’ar hannu amma mutum 70 ne kadai suka amfana da tallafin tun daga wancan lokacin.

A wani labarin kuma Majalisar Zartarwar Nijeriya ta amince da karbo lamunin gata na dala biliyan daya daga Bankin Raya Kasashen Afirka 

Advertisement

Gwamnatin tarayya ta ce yanzu haka shirye-shirye sunyi nisa domin sauya akalar motoci har milyan 10 masu amfani da man fetir zuwa amfani da Gas nan da watanni 36 masu zuwa.

Karaminin ministan Mai, Ekperikpe Ekpo ne ya baiyana haka a yayin baje kolin mai da iskar gas na shekarar bana wanda ake gudanarwa a birnin Abu Dhabi na hadaddiyar daular larabawa.

Advertisement

A wata sanarwa da kakakinsa Louis Ibah ya fitar, ya baiyaan cewar a yanzu haka anyi kawance da kanfanoni masu zaman kansu domin kawo kayayyakin da za’a yi amfani dasu wajen sauya akalar motocin nan da watanni 9 masu zuwa.

Ya ce matakin wani yunkuri ne na inganta yin amfani da Gas a tsakanin motocin kasar a maimakon Man fetir da suka dogara dashi.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending