Connect with us

News

Kotun daukaka kara Tace Zaɓen Dan Majalisar Kunchi/Tsanyawa Bai Kammala ba

Published

on

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

 

Advertisement

Kotun daukaka kara da ke Abuja ta yi watsi da hukuncin da kotun sauraron kararrakin zabe ta Majalisar Dokoki ta kasa da ta jihar Kano ta yanke.

Jaridar Inda Ranka ta rawaito cewa a baya kotun ta tabbatar da nasarar ga Garba Ya’u Gwarmai na jam’iyyar APC, Inda ta ce shi ne ya lashe zaben majalisar dokokin jihar na kananan hukumomin Kunchi/Tsanyawa ba dan takarar jam’iyyar NNPP Muhammad Yusuf Maigado ba.

Advertisement

Yan sanda  sun cafke wasu mutane takwas da ake zargi da yin garkuwa da mutane a Jihar Kaduna 

Bugu da kari, kotun daukaka kara ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) da ta sake gudanar da zabe a rumfunan zabe inda aka soke ƙuri’u ko kuma aringizon kuri’u cikin kwanaki 90 daga ranar da za a yanke hukunci kamar yadda Majiyar Kadaura24 justice watch ta rawaito.

 

Advertisement

Idan za’a iya tunawa tun bayan da hukumar zabe ta INEC ta ayyana Gwarmai a matsayin wanda ya lashe zaben, lauyan masu shigar da kara, Barista Abba Hikima, ya nuna rashin jin dadinsa inda ya kai karar kotu .

Hikima ya kara da cewa INEC ta tafka kura-kurai a shari’a ta hanyar bayyana sakamakon zabe a lokacin da ba a kammala zaben ba, kuma an tafka kura-kurai da dama da suka hada da soke sakamakon zabe, lalata akwatunan zabe, da kuma kura-kurai daban-daban na zabe.

Advertisement

 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending