Connect with us

News

Gwamnan Jihar Sakkwato Ya Gabatar Da Kasafin Kudin 2024 Na Biliyan 270

Published

on

Gwamna Ahmed Aliyu na Jihar Sakkwato

DAGA MUHAMMAD MUHAMMAD ZAHRADDIN

Gwamna Ahmed Aliyu na Jihar Sakkwato a yau Juma’a ya gabatar da daftarin kudurin kasafin kudin shekarar 2024 na naira biliyan 270 a gaban majalisar dokokin jihar domin amincewa.

A cewar gwamnan kasafin kudin sabuwar shekarar na da manufar tabbatar da muradun al’umma a fadin jihar na wanzar da kudurorin gwamnatinsa na raya jiha ta kowane irin fanni.

CBN Zai Haramta Harkokin Kudi A Asusun Bankin Da Babu BVN Da NIN A 2024

A kasafin na 2024, kudin manyan ayyuka sun kama naira biliyan 90, 640, 286 a yayin da kudaden al’amurran yau da kullum suka kama naira biliyan 46, 923, 537, sai kudaden gudanarwa naira biliyan 50, 938, 232.

 

Fannin ilimi ya samu kaso mafi yawa na naira biliyan 42, 868, 402, sai fannin lafiya da ke biye da naira biliyan 31, 014, 441, a yayin da ma’aikatar ayyuka ta samu naira biliyan 18, 807, 208, sai fannin aikin gona da ke da naira biliyan 10, 252, 388 wanda ya hada da samar da nau’ukan abinci ga al’umma da takin zamani da kayan aikin gona ga manoma.

Advertisement

 

Gwamnan ya bayyana cewar gwamnatinsa ta yi tanadi na musamman ga tallafa wa al’umma a kasafin kudin tare da yaki da fatara da karfafawa mata da matasa domin ganin sun zamo masu dogaro da kai.

Leadership ta ruwaito cewa A jawabinsa, shugaban majalisar dokoki ta jiha, Honarabul Tukur Bala ya tabbatarwa da gwamnan cewar majalisar za ta dukufa ga aikin tabbatar da kasafin kudin domin samun nasarar kudurorin gwamnatinsa.

A wani labarin kuma CBN Zai Haramta Harkokin Kudi A Asusun Bankin Da Babu BVN Da NIN A 2024

Gwamnatin Najeriya ta fara ɗaukar matakan rage cunkoson gidajen gyaran hali da ke ɗaukacin faɗin ƙasar, inda taƙaddamar da shirin a jihar Kano.

Gwamantin ta ce soma da mutum ɗari ne gwamanti ta bi yawa tarar, wanda dukkansu masu ƙananan laifuka ne da waɗanda suke farkon zuwa ne gidan.

Advertisement

Haka kuma ta ce akwai mutum sama da 4,000 da ake buƙatar a fitar da su daga gidajen gyaran halin ƙasar, sannan za a kawar da cinkoson da ake fama da shi a gidajen.

Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending