News
Rundunar Ƴan sanda sun kama dillalan muggan makamai mutum uku
DAGA UMAR IBRAHIM HOTORO
Rundunar ‘Yan Sandan Filato ta bayyana damƙe mutane uku da ake zargi da safarar muggan makaman da aka yi rikicin kashe-kashe da su a ranar 24 ga Disamba, 2023
A mumnunan harin dai wanda aka kai daren jajibirin Kirsimeti, an kashe sama da mutum 100, tare da jikkata wasu da yawan gaske.
Me ya sa Tiwa Savage ta nemi ‘yan sanda su shiga tsakaninta da Davido
An kai munanan hare-haren a yankunan ƙananan hukumomin da suka haɗa da Barikin Ladi da Ɓokkos.
Har yanzu babu wata kungiyar da ta fito ta ɗauki nauyin kai harin wanda aka kai cikin dare, a Filato, jihar da aka yi asarar dubban mutane a rikice-rikicen ƙabilanci da na addini daban-daban a baya.
Premium Times ta ruwaito cewa Kakakin ‘Yan Sanda Olumuyiwa Adejobi, ya sanar da kama waɗanda ake zargi da safarar manyan bindigogi, a taron manema labarai da ya kira a Abuja.
Ya ce an samu nasarar cafke waɗanda ake zargin bayan Sufeto Janar na ‘Yan Sanda Kayode Egbetokun ya ce a bi hanyoyin sirri a gano kuma a kamo masu hannu a mummunan kisan.
Ya ce an kama wata mota ƙurar Golf da zabgegiyar AK-47 da albarusai 1,000 da jigida biyar a hannun waɗanda ake zargin.
Ya ce ana ci gaba da ƙoƙarin kamo sauran da ake zargin da hannun su a kashe-kashen.
Ya ce akwai kuma wasu masu manyan laifukan da aka kama tun a ranar 13 ga Disamba, bisa kisan mutum uku Gaude, a yankin Kuje.
A wani labarin kuma Me ya sa Tiwa Savage ta nemi ‘yan sanda su shiga tsakaninta da Davido
Babban Bankin Najeriya CBN ya sauya matsayarsa kan hada-hada da kuɗin intanet ko kuma cryptocurrency a ƙasar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata sanarwa da bankin ya fitar ranar Juma’a da ke umartar bankunan kasuwanci na Najeriya cewa su yi watsi da haramcin da ya saka kan amfani da kuɗin na crypto tu a 2021.
CBN ya ce yadda ake yayin kuɗin na crypto yanzu a faɗin duniya ya nuna irin buƙatar da ake da ita ta saka dokoki a kan sa.
“A watan Fabarairun 2021 CBN ya haramta wa bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi amfani da cryptocurrency saboda almundahanar kuɗi da kuma ɗaukar nauyin ta’addanci,” in ji sanarwar.
“Sai dai kuma, abin da ke faruwa a duniya ya nuna cewa akwai buƙatar a kula da dukiyoyin hada-hada ta intanet wato Virtual Assets Service Providers (V/ASPs).”
Ya ƙara da cewa hukumar kula da hada-hada da hannayen jari za ta fitar dokoki da sharuɗɗan amfani da dukiyoyoin intanet ɗin.
Amma babban bankin ya jaddada haramcin yin kasuwanci, ko kuma mallakar asusun crypto ga bankunan kasuwancin su da kansu
